Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-16 16:58:32    
Kungiyar kasashen 'yan-ba-ruwanmu tana zura ido wajen yin gyare-gyare da kanta da moriyar kasashe masu tasowa

cri

A cikin taron koli, za a yi tattaunawa kan batun Palesdinu, da batun kasar Sudan, da batun nukiliya na kasar Iran, da rikicin kasar Honduras da sauran manyan harkokin duniya. Kuma yadda kungiyar NAM za ta iya taka muhimmiyar rawa da kuma ba da gudummawa wajen daidaita matsaloli da kiyaye zaman lafiya a duniya ya zama wani muhimmin aiki na wannan taron koli. Sabo da haka, taron koli zai yi tattaunawa wajen kafa wata sakateriya domin sa ido kan ayyukan gudanar da kudurin da aka yi cikin taron koli, da kara karfin daidaito tsakanin membobin kasashen kungiyar. Ban da haka kuma, za a yi tattaunawa wajen zabi wasu mutanen da ke da ilmin harkokin duniya daga membobin kasashen kungiyar domin kafa wani rukunin mutane masu ilmi, wadannan mutane za su daidaita matsayin membobin kasashen kungiyar, da kuma ba da shawara wajen daidaita matsaloli.

Masu bincike suna ganin cewa, a cikin yanayin zaman lafiya da neman bunkasuwa da ake ciki a yanzu, dole ne kungiyar ANM ta daidaita manufofin da take tafiyarwa cikin lokaci domin dacewa da sabon zamani. Kuma idan tana son kara taka muhimmiyar rawa kan harkokin duniya, dole ne ta kara kiyaye moriyar kasashe masu tasowa. [Musa Guo]


1 2 3