Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-16 16:58:32    
Kungiyar kasashen 'yan-ba-ruwanmu tana zura ido wajen yin gyare-gyare da kanta da moriyar kasashe masu tasowa

cri

A wannan rana, shugaban Muhammad Hosni Mubarak na kasar Masar wanda ya zama sabon shugaban kungiyar NAM ya yi jawabi cewa, ya kamata kungiyar NAM ta saba da sabon yanayin da ake ciki. Ya ce, a cikin shekaru da yawa bayan da aka kafa kungiyar NAM, an sami canje-canje sosai a duniya, an riga an shiga sabon zamani na dogara da juna, tare da samun canje-canje da dama. Ya kamata membobin kasashen kungiayr NAM su kara hada kansu domin tinkarar matsaloli tare, da sa kami ga kungiyar NAM da ta kara taka rawa kan harkokin kiyaye zaman lafiya, da zaman karko a duniya.

Yawancin membobi kasashe 118 na kungiyar NAM su ne kasashe masu tasowa. Neman bunkasuwa shi ne muhimmin aikinsu na dogon lokaci. A cikin yanayin tabarbarewar tattalin arziki da matsalar hada-hadar kudi ta haddasa a yanzu, taron koli na kungiyar NAM ya zura ido kan kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da kara yin hadin gwiwa tsakaninsu. A cikin jawabinsa, Mr. Mubarak yana fata za a kara yin hadin gwiwa, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, musamman ma moriya kasashe mafi talauci na Afirka. Kuma ya kira a kafa wani sabon tsarin siyasa, da tattalin arziki da ciniki na duniya wanda ya fi adalci da daidaito domin samun moriyar dukkan kasashen duniya.

A wannan rana, Mr. Ban Ki-moon babban sakatare na majalisar dinkin duniya ya yi jawabi, inda ya yi kira ga kasashe masu ci gaba da su cika al'kawarinsu na ba da taimako ga kasashe masu tasowa.

1 2 3