Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-02 10:49:00    
Taron koli na AU na mai da hankali kan batun bunkasa ayyukan gona da kuma halin da ake ciki a Somaliya da dai sauran muhimman batutuwa

cri

Aminai 'yan Afrika, taron kolin da ake gudanarwa ya kuma fi dora muhimmanci kan yanayin da ake ciki yanzu a kasar Somaliya da kuma sauran wassu muhimman batutuwa. Game da batun Somaliya, shugaban kungiyar AU, Mista Jean Ping ya yi jawabi a gun taron, inda ya fadi cewa, yanzu haka, kasar Somaliya na fuskantar babban kalubale wajen tabbatar da samun zaman lafiya da kuma sulhuntawar al'ummomi. ' Idan kasa da kasa ba su dauki tsauraran matakai cikin lokaci ba, to kuwa mai yiwuwa ne Somaliya za ta sake fada cikin halin kara-a-zube da kuma rikice-rikicen da ake yi tsakanin kungiyoyi da rukunoni daban-daban, wadanda suka ki ci suka ki cinyewa.

Batun kafa hukumar iko ta AU yana daya daga cikin wassu muhimman batutuwan da za a tattauna a kai a gun taron. Mista Jean Ping ya ce, mayar da zaunanniyar hukumar kungiyar tarayyar kasashen Afrika wato AU wato kwamitin kawancen kasashen Afrika wato AU a matsayin wata hukumar iko ta kawancen, ya kasance babban buri ne na jama'ar Nahiyar Afrika. Kazalika, Mista Jean Ping ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Afrika su kara yin hadin gwiwa da daidaitawa tsakaninsu, da gaggauta yunkurin tabbatar da samun bunkasuwar harkokin siyasa da na tattalin arziki na bai daya, ta yadda za a dukufa kan kafa wata hadaddiyar Nahiyar Afrika. ( Sani Wang )


1 2 3