Mataimakin shugaban kungiyar AU Mista Mwencha ya yi jawabi a gun taron, inda ya yi nuni da cewa, tun daga farkon shakarar bara ne, aka samu saurin karuwar farashin abinci a fadin duk duniya. Hakan ya janyo babban kalubale ga kokarin da kasashen Afrika suke yi wajen kawar da talauci. Sa'annan ya furta cewa, ' Cikakken shirin bunkasa ayyukan gona na Afrika' da kungiyar AU ta kaddamar da zummar taimakawa kasashen Afrika wajen bunkasa sha'anin noma da kuma Afrikawa dake fama da talauci, labuddah zai bada muhimmin taimako irin na jagoranci ga warware tarzomar abinci. Dadin dadawa, Mista Mwencha ya kalubalanci gwamnatocin kasashe daban-daban na Afrika da su aiwatar da wannan shiri cikin tsanaki, ta yadda za su tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.
1 2 3
|