Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 16:08:55    
Kasar Sin ta kara sanya muhimmanci kan aikin kare kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya

cri

Kamar yadda Xu Chuzhu da 'dansa Xu Qiang suka yi, wasannin fasaha na gargajiya na kasar Sin sun samu cigaba a iyalai daban daban daga zuri'a zuwa zuri'a. Amma, a lokacin zamani, zaman rayuwar mutane sun samu sauyawa sosai, akwai ayyuka iri-iri da yawa da matasa suka iya zaba, wannan ya kawo cikas ga cigaban wasannin fasaha na gargajiya, matasa sun rasa nuna sha'awa ga wadannan wasannin fasaha, wasu wasannin fasaha na gargajiya sun bace.

Gundumar Yongkang ta lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin ta shahara sabo da kayayyakin gwangwani, a lokacin da, akwai mutane da yawa da suka kera kayayyakin gwangwani a gundumar, amma a shekarun baya, tsoffi sun riga mu gidan gaskiya, an rasa mutanen da za su gaji fasahar kera kayayyakin gwangwani. Shugaban cibiyar kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya na yankin Yang Biao ya ce, "Mutanen gundumar Yongkong su kan gudanar da kamfannoninsu, amma koyon fasahar kera kayayyakin gwangwani yana bukatar shekaru 3, matasa ba su son koyon wannan fasaha sabo da su kan sha wahalhalu da yawa, ban da haka kuma, ba za su samu riba sosai ba."

Kayayyakin gwangwani suna kusan bacewa, amma mutanen gundumar Yongkang ba su mai da hankali a kan wannan hadarin al'adu. A sakamakon kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi a cikin shekaru gomai, jama'ar Sin suna kara sanya muhimmanci kan aikin kare kayayyakin gargajiya.

Gwamnatin kasar Sin ta bayar da jerin manufofi don kalubalantar mutane da su gada fasahohin kera kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya, sannan kuma, ta ci gaba da kyautata shari'un dake da dangane da kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya, ana kokarin kafa tsarin kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya na gundumomi da birane da larduna da kuma duk kasar. A sa'i daya kuma, duk mutanen kasar Sin sun sanya muhimmanci kan yadda za a gaji fasahohin gargajiya da kyau a zamani.

Peng Huiheng ta koyar da wani irin wakar da ake kira "Bangzi" a wani kwaleji dake lardin Hebei, ta koyi wannan irin waka daga wajen wani kwararre na lardin Hebei, sannan ta rera wakar a kungiyar 'yan wasanni cikin shekaru da yawa, yanzu, ta koya wa dalibanta fasahar rera wakar. Peng Huiheng ya bayyana cewa, a kan shan wuya a yayin da ake koyon wakar "Bangzi", shi ya sa, yawan matasan da suke son koyon wakar ya ragu sosai. Haka kuma, shahararrun wakokin "Bangzi" suna kusan bacewa. Peng Huiheng ta shawarci gwamnati da ta kara nuna goyon baya ga ba da ilmin wakar "Bangzi" da tsara wakoki masu dadin ji, ta ce, "A ganina, ba da ilmin wakoki iri na gargajiya ya yi daidai da mafarin kogi, ya kamata a kara gayyatar malamai dattijan rera wakokin gargajiya don yada wadannan wakoki."

Kwararru da masana suna ganin cewa, idan an kwatanta da kasashe masu cigaba, kasar Sin ta makara da fara aikin kare kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya, ana bukatar ci gaba da kyautata wannan aiki. Nan da shekaru da yawa, kasar Sin za ta samu babban cigaba a fannin kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya, wadannan wasannin fasaha na gargajiya za su sake farfadowa a nan gaba.


1 2 3