Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 16:08:55    
Kasar Sin ta kara sanya muhimmanci kan aikin kare kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya

cri

A ran 13 ga wata ranar kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya ta hutu ce ta kasar Sin, a ran 11 ga wata, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta nada magadan kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya na matakin uku. Tun daga shekarar 2006 da gwamnatin kasar Sin ta tsara ranar kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya, jama'ar Sin sun kara mai da hankali kan kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya. Yanzu, yadda za a gaji kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya daga zuri'a zuwa zuri'a ya zama abin da ya fi jawo hankalin mutanen kasar Sin. To, bari mu sauraro wani babi na wasan kwaikwayo na 'yar tsana mai zare. Ga shi.

Mr. Xu Zhuchu dake da shekaru 70 da haihuwa shi ne magajin 'yar tsana mai zare na zuri'a ta 6 dake birnin Zhangzhou na lardin Fujian, ya sassaka mutum-mutumi iri daban daban a kan ice da wuka. An taba dauki 'yar tsana mai zare da Xu Zhuchu ya kera zuwa kasashen Amurka da Singapore da Koriya ta kudu da Japan da da kuam Australia da sauran kasashe da yankuna da yawa don yin nune-nune, kuma gidan kayan gargajiya na kasashe fiye da 50 sun ajiye 'yar tsana mai zare nasa. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta taba mika wa shugabannin kasashen waje 'yar tsana mai zarensa a matsayin kyauta masu daraja.

A kwanakin kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya a karo na biyu na shekarar 2007, Xu Zhuchu da 'dansa Xu Qiang sun halarci nune-nunen kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya na kasar Sin a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya je kallon nune-nunen 'yar tsana mai zarensu, ya yaba wa fasaharsu ta sassaka 'yar tsana mai zare, kuma ya yi kira da su gaji wannan fasaha daga zuri'a zuwa zuri'a da kuma yada fasaharsu.

1 2 3