Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 16:08:55    
Kasar Sin ta kara sanya muhimmanci kan aikin kare kayayyakin tarihi na al'adu na gargajiya

cri

Xu Zhuchu ya yi tsammani cewa, suna shan wuya sosai wajen gada wannan fasaha daga kakani-kakaninsu, ya kamata ya yi kokarin ci gaba da raya wannan fasaha. Sabo da haka, ya soke ka'idar gargajiya ta gidansa. Ya ce,"A lokacin da, mun koya wa mazan gidanmu wannan fasaha, amma kada mu koya wa mata. Amma, yanzu, yarinyata ta iya wannan fasaha, na koya musu. A ganina, yanzu, maza da mata suna kan matsayi daidai a cikin zaman al'umma. A lokacin da, an hana yaduwar fasahohinsu don kaucewa raguwar moriyarsu, amma yanzu, gwamnati ta tsara kyakyawar munufa wajen kiyaye moriyarmu, muna da albashi, ba mu damu da rashin aikin yi da karancin abinci ba."

A shekarar 1996, Xu Zhuchu da 'dansa sun kafa wani gidan nune-nunen wasan fasahar 'yar tsana mai zare a birnin Cangzhou, duk da cewar fadinsa ya kai muraba'in mita 200 kawai, amma ya jawo mutane masu dimbin yawa da suka nuna sha'awa kan wasan fasaha na 'yar tsana mai zare na kasashen waje da yankunan duniya da yawa.

Ban da wannan kuma, Xu Zhuchu da 'dansa suna kokarin shigar da wasan 'yar tsana mai zare zuwa makaranta don kara wa yara sani na wannan wasan fasaha. 'Dansa Xu Qiang yana ci gaba da nazari kan wasan 'yar tsana mai zare don mai da shi a matsayin wani sana'a. Xu Qiang ya koyi fasahar kera 'yar tsana mai zare daga wajen mahaifinsa har shekaru gomai, shi ne magajin wannan fasaha a zuri'a ta 7 na iyalai, yana kaunar wasan 'yar tsana mai zare sosai. Ya ce, "Na fara koyon wasan 'yar tsana mai zare tun daga ina da shekaru 9 da haihuwa, na gaji aikin mahaifina kafin shekaru fiye da 20 da suka gabata. Daga farko, na taimaki mahaifina kawai, amma na fara sha'awa ga wannan wasan fasaha, ya kamata mu raya da gaji wannan wasan fasaha."

1 2 3