Ban da wannan kuma, taron zai tattauna kan yadda za a aiwatar da shirin tattaunawa a tsakanin Afirka da kungiyar tarayyar Turai wato EU. Yayin da shugaban kwamitin kungiyar AU Jean Ping ke yin ziyara a kasashen Turai a kwanan nan, ya taba furta cewa, dole ne Afirka da Turai su kulla huldar abokantaka a tsakaninsu, tarihi da al'adu da kuma makwabta a fannin yankunan kasa sun hada Turai da Afirka tare, kuma Afirka na bukatar kudin da Turai ta kebe a fannin raya muhimman ayyukan yau da kullum da sufurin kayayyaki da cinikayya da ayyukan ba da hidima da kuma makamashi.
Ban da wadannan muhimman batutuwa biyu da za a tattauna a kai a yayin taron, za a tattauna kan yadda za a tsugunar da 'yan gudun hijira da kuma komawarsu cikin gida, wadanda suka bar gidajensu sakamakon yaki da hargitsi, da kuma yadda za a aiwatar da makasudin samun bunkasuwa da MDD ta tsara a shekara ta 2000.(Kande Gao) 1 2 3
|