Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-30 17:31:06    
Taron koli na kungiyar AU zai sanya muhimmanci kan ayyukan gona da kuma tsaron kai

cri

A fannin raya ayyukan gona, ko da yaushe kasashen Afirka su kan fuskanci matsalar karancin fasahohin yin ban ruwa da rashin hanyoyin tafiye-tafiye da kuma karancin kudi. Ko da yake gwamnatoci na kasashe daban daban na Afirka sun taba yin alkawarin cewa, yawan kudin da ya kamata a kebe a kan raya ayyukan gona da kauyuka ya kai a kalla kashi 10 cikin kashi dari bisa na dukkan kasafin kudi, amma ya zuwa yanzu kasashen Afirka shida ne kawai suka cimma wannan buri, yawan kudin da akasarin kasashen Afirka ke kebewa a wannan fanni kuma bai wuce kashi 5 zuwa kashi 6 cikin kashi dari kawai ba. Abin da ya fi tsanani shi ne hauhawar farashin hatsi na duniya wadda ta sa 'yan Afirka miliyan 28 suka shiga mawuyacin hali na fama da talauci, har ma hakan ya sa an ta da hargitsi sau da yawa a kasashen Afirka da dama sakamakon batun hatsi.

Tsaron Afirka wani muhimmin batu ne na daban da za a tattauna a kai a yayin taron. Shugabannin da za su halarci taron za su tattauna kan inganta amfanin kungiyar AU domin hana da kuma warware rikice-rikice da kuma al'amuran tashin hankali da aka samu a kasashen Afirka sakamakon zabe. Manazarta sun nuna cewa, matsalar siyasa ta kasar Madagascar za ta zama muhimmin batun da za a tattauna a kai a yayin taron.

1 2 3