Shugabannin kasashe membobin kungiyar tarayyar Afirka wato AU za su taru a birnin Sirte na kasar Libya da ke bakin teku daga ran 1 zuwa ran 3 ga wata mai zuwa domin halartar taron koli a karo na 13 na kungiyar AU, wanda za a mayar da "sa kaimi ga karuwar tattalin arziki ta hanyar zuba jari a kan ayyukan gona da kuma tsaron shiyya-shiyya" a matsayin babban takensa.
A cikin rahoton tattalin arzikin Afirka na shekara-shekara da kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD da kuma kungiyar AU suka bayar, an kiyasta cewa, a shekarar da ake ciki, jimillar karuwar tattalin arzikin Afirka za ta ragu daga kashi 5.1 cikin kashi dari na shekara ta 2008 zuwa kashi 2 cikin kashi dari, amma ayyukan gona za su samar da kyakkyawar dama ga Afirka wajen fama da talauci. Haka kuma rahoton ya yi kira ga kasashen Afirka da su kara sanya muhimmanci kan ayyukan gona da kuma kara zuba jari a wannan fanni. Mayar da batun zuba jari a kan ayyukan gona a matsayin babban taken taron ya nuna muhimmin matsayin ayyukan gona a fannin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin Afirka da kuma cimma burin samun bunkasuwa da MDD ta tsara a shekara ta 2000.
1 2 3
|