
A cikin jawabinsa, shugaban Rasha, Dmitry Medvedev ya bayyana cewa, ya kamata kasashen hudu su kara daidaita matsayinsu da juna, kuma su gabatar da shawarwari a kan manyan batutuwan kudi na duniya, su tabbatar da daidaiton da aka cimma a gun taron kolin G20 da aka yi a Washington da kuma London, su kyautata tsarin kudi na duniya. Sa'an nan kuma, su inganta hadin gwiwa a tsakanin sassa da dama da kuma sassa bibiyu, don tinkarar matsalolin samar da isashen makamashi da abinci da kuma sauyin yanayi. Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula Da Silva shi ma cewa ya yi, matsalar kudi da duniya ke fama da ita ta fahimtar da kasa da kasa a kan muhimmancin kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa, kuma hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen hudu na iya bunkasa sosai. Har wa yau kuma, firaministan kasar Indiya, Manmohan Singh ya ce, kamata ya yi kasashen hudu su tsaya ga nuna kin jinin kariyar ciniki, kuma su habaka hadin gwiwarsu ta fannonin kimiyya da fasaha da makamashi da kuma ayyukan gona. (Lubabatu) 1 2 3
|