Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 18:18:29    
Ganawa ta farko a tsakanin shugabannin kasashen BRIC

cri

A cikin jawabinsa, Mr.Hu Jintao ya kuma gabatar da shawarwari kan yadda kasashen hudu za su yi domin tinkarar matsalar kudi ta duniya da farfado da tattalin arzikin duniya. Ya ce, kamata ya yi kasashen hudu su dauki matsayin gaba wajen farfadowa daga matsalar kudi da ke galabaitar da kasashen duniya. Na biyu, su dukufa a kan gyare-gyaren hukumomin kudi na duniya, su sa kaimi da a tsara shirin gyaran asusun ba da lamuni na duniya da bankin duniya, don kara wakilcin kasashe masu tasowa da kuma daga matsayinsu. Na uku, ya kamata a dukufa a kan tabbatar da shirin bunkasuwa na shekarar 2000 na MDD, wato MDGs, su ci gaba da yin kira ga kasa da kasa da su mai da hankali a kan illolin da matsalar kudi ke haddasa wa kasashe masu tasowa, su kalubalanci kasashe da suka ci gaba da su cika alkawuransu na ba da taimako ga kasashe masu tasowa. Na hudu, a lokacin da ake fuskantar matsalar kudi ta duniya, kamata ya yi su yi hangen nesa, su daidaita sauran matsalolin da ke shafar bunkasuwa yadda ya kamata.

1 2 3