Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 15:42:45    
An samu sakamako mai kyau a fannin gudanar da aikin kare babbar ganuwa

cri

Dadin dadawa, kwararru sun bayyana cewa, rukunin nazarin babbar ganuwa su ma sun yi bincike kan halin da babbar ganuwa ke ciki, kuma sun samu hakikannan bayanai da yawa. Wadannan sakamakon da suka samu za su ba da babbar gundummawa ga aikin tsara shirin kare babbar ganuwa.

Shugaban hukumar kayayyakin tarihi ta kasar Sin Shan Jixiang ya bayyana cewa, sabo da dogon tarihi da sauyawar zaman al'umma, babbar ganuwa tana fuskantar kalubale daga indalahi da mutane sosai. A cikin tarihi, rikice-rikice da ambaliyar ruwa sun taba halaka babbar ganuwa. Haka kuma, mazauna wurin dake dab da babbar ganuwa sun cire bulon babbar ganuwa don yin amfani da su wajen gina gidaje. Shan Jixiang ya kara da cewa,"Kalubale mafi girma da muke fuskanta shi ne sauyawar yanayi da kara gina gine-gine."

Ka'idojin kare babbar ganuwa da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2006 sun kayyade cewa, dole ne a yi aikin kare babbar ganuwa mai tsattsaura, kada a ratsa babbar ganuwa don gina hanyoyi da gine-gine. Kwararre a fannin kare babbar ganuwa Luo Zhewen ya ce, "A ganina, za a yi aikin kare babbar ganuwa mai kyau ta hanyar yin nazari."

An labarta cewa, aikin yin nazari kan babbar ganuwa ta daular Ming mataki na farko ne na aikin yin nazari kan babbar ganuwa ta kasar Sin. Daga baya, za a yi nazari kan babbar ganuwa ta daulolin Qin da Han da sauran dauloli. Sarki na farko a cikin tarihin kasar Sin Qin Shihuang ya gina babbar ganuwa ta daular Qin, tarihinta ya kai shekaru dubu 2 da dari 2. Bayan sarkin Qin Shihuang, babbar ganuwa da aka gina a lokacin daular Han sashe daya na babbar ganuwa mafi girma ne a cikin tarihin kasar Sin.

Bisa shirin aikin da hukumomin da abin ya shafa suka tsara, an ce, ya zuwa karshen shekara mai zuwa, za a tabbatar da abubuwan duk sassan babbar ganuwa. Sannan kuma, za a tsara shirin kare babbar ganuwa da kafa dokoki a gare ta. (Lami)


1 2 3