Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 15:42:45    
An samu sakamako mai kyau a fannin gudanar da aikin kare babbar ganuwa

cri

 Shahararriyar babbar ganuwa ta kasar Sin ita ce gini mafi tsawo na tarihi a fannin aikin soja. Tsawon babbar ganuwa ya kai nawa ne? Amma ba a tabbatar da hakikanin tsawonta ba a cikin dogon tarihi. A kwanakin baya ba da dadewa ba, hukumar kayayyakin tarihi ta kasar Sin da hukumar tsara taswira ta kasar sun sanar da tsawon babbar ganuwa ta daular Ming wanda ya kai kilomita 8851.8. Wannan karo na farko ne da kasar Sin ta sanar da hakikanin tsawon babbar ganuwa ta daular Ming. Tabbatar da tsawon babbar ganuwa wani aiki ne na aikin kare babbar ganuwa na kasar Sin, wannan adadin da aka samu ya shaida cewa, an samu sakamako a fannin kare babbar ganuwa a wannan mataki, kuma ya aza harsashi ga gudanar da aikin kare babbar ganuwa. Yanzu ga cikakken bayani.

An fara gina babbar ganuwa a karni 8 zuwa 7 B.C, daga baya, an ci gaba da gina da gyara ta har shekaru dubu biyu ko fiye, mutanen dauloli daban daban sun yi ta yi wannan aiki, babbar ganuwa ta shafi larduna da jihohi da birane da yawa. Wani sashen babbar ganuwa da aka gina shi ne daga karni 14 zuwa karni 16 wato lokacin daular Ming sashe mafi girma da inganci a tarihi, adadin da aka gabatar a wannan karo shi ne tsawon sashen babbar ganuwa na daular Ming.

A cikin tarihi, ba wanda ya san hakikanin tsawon babbar ganuwa. Sinawa su kan kiranta babbar ganuwa ta tsawon Li dubu 10, wannan "li" wani ma'aunin tsawon hanya na kasar Sin ne, li dubu 10 ya yi daidai da kilomita dubu 5, jama'ar Sin su kan siffanta cewa, babbar ganuwa tana da tsawo sosai da sosai. Kwararren nazari babbar ganuwa kuma shugaban kwamitin masanan babbar ganuwa na kasar Sin Luo Zhewen ya ce,

"A cikin shekaru dubu 2 da suka gabata, an yi ta yi gina da gyara babbar ganuwa. Bisa bayanan da aka yi a da, an ce, tsawon babbar ganuwa ya kai kilomita dubu 50, wanda ba a taba ganin wannan irin gini a duniya ba. Ban da haka kuma, babbar ganuwa tana da ma'anar tarihi sosai. Babbar ganuwa ta zama wani littaffin tarihin mulkin danniya, ta bayyana sauyawar mulkin danniya na kasar Sin, kuma ita ce sakamakon da jama'ar kabilu daban daban na kasar Sin suka samu wajen aiki cikin dogon lokaci."

1 2 3