Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 15:42:45    
An samu sakamako mai kyau a fannin gudanar da aikin kare babbar ganuwa

cri

Tare da kokarin da jama'ar Sin suka yi wajen gyara ta a cikin shekaru dubu 2 ko fiye, babbar ganuwa ba ta taba rushewa ba, a zukatan jama'ar Sin, babbar ganuwa ba wani ginin tarihi kawai, amma ta wakilci tunanin al'ummar kasar Sin. Akwai wani karin magana na kasar Sin da cewa, wanda bai taba hau kan babbar ganuwa ba, to shi ba wani namijin gaske ba. Ban da haka kuma, babbar ganuwa ta iya kalubalatar jama'ar Sin da su nemi samun bunkasuwa da yi kokarin aiki. Sabo da haka, aikin kare babbar ganuwa ya jawo hankalin duk jama'ar kasar Sin. Mr. Luo Zhewen dake da shekaru 85 da haihuwa ya taba halartar aikin kare babbar ganuwa a shekarun 50 na karnin da ya wuce. Kuma a wancan lokaci, Jamhuriyar jama'ar kasar Sin da ta kafu ba da dadewa ba ta riga ta daukar matakai iri daban daban don kare babbar ganuwa.

A cikin shirin kare babbar ganuwa da kasar Sin ke gudanar daga shekarar 2005 zuwa shekarar 2014, za a kammala ayyukan nazari da tsara shirin kare babbar ganuwa da kayyade yankin da za a kare shi da ceton muhimman zanguna na babbar ganuwa. Daga cikinsu, aikin da ya fi kan gaba shi ne nazari kan babbar ganuwa.

A shekarar 2007, hukumar tsara taswira da hukumar kayayyakin tarihi na kasar Sin sun fara gudanar da aikin gwada tsawon babbar ganuwa ta daular Ming, a cikin shekaru 2 da suka gabata, ma'aikata darurruwa sun gwada tsawon babbar ganuwa da kuma yin aikin nazari kan kayayyakin tarihi da halin dake kewayanta a cikin larduna da jihohi masu cin gashin kansu da birane 10. Mataimakin babbar injiniya ta kolejin gwada da tsara fasali na Beijing Wang Lei ya bayyana cewa,

"Mun gwada babbar ganuwa ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani da kimiyya. Mun hau kan tsaunuka masu tsayi don tabbatar da mafari da kuma zangon karshe na babbar ganuwa. Mun sha wuya sosai don yin wannan aiki."

Bayan jerin aikin gwada da aka yi, an tabbatar da cewa, babbar ganuwa ta daular Ming ta fito ne daga tsaunin Hushan na lardin Liaoning dake gabashin kasar Sin zuwa matsatsar Jiayuguan ta lardin Gansui dake yammacin kasar. Daga gabas zuwa yamma, ta ratsa gundumomi 156 na larduna da jihohi masu cin gashin kansu da birane 10, tsawonta ya kai kilomita 8851.8.

Ban da wadannan kuma, an samu gine-gine da kayyayakin tarihi na babbar ganuwa ta daular Ming, wadanda yawansu ya kai 498, alal misali, ramin kona abubuwa da kuka da aka gano da birnin Tianjin, da kuma bangon duwatsu na gargajiya da aka samu a birnin Beijing.

1 2 3