Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-15 17:00:50    
Kasuwar sayar da motoci a kauyuka ta samu ci gaba cikin sauri

cri

Yawan motocin da ake sayar da su a kasuwar kauyuka ya fi kamfanonin kera motoci wadanda suka yi hasashe da yawa. Ba ma kawai kamfanonin kera kananan motoci suna namijin kokarin kera karin kananan motoci domin tabbatar da samar da isassun motocin da ake bukata a kauyuka ba, har ma wasu kamfanonin da suke kera motocin kawa sun kuma zura idonsu kan kasuwar kauyuka. Alal misali, kamfanin kera motoci na Chery, wato kamfanin kera motoci na kasar Sin wanda ke da tamburin nasa mafi shahara yana kuma kokarin samar da kananan motocin da suke dacewa da muhallin kauyuka. Mr. Jin Gebo, mataimakin babban direktan kamfanin sayar da motocin Chery ya gaya wa wakilinmu cewa, a farkon shekarar da ake ciki, kamfanin Chery ya soma sayar da kananan motoci a kasuwar kauyuka. Mr. Jin ya bayyana cewa, "Kananan motocin da muke sayarwa a kauyuka suna shafar wani sabon samfuri, wato suna iya dacewa da halin da ake ciki a garuruwa da kauyuka baki daya. A waje daya, muna mai da hankali kan mutane wadanda suke aiki a garuruwa, amma yanzu sun koma kauyukansu tare da kudin da suka samu a birane. Mai yiyuwa ne za su sayi motoci domin tafiyar da harkokin sufurin kayayyaki ko fasinjoji. Wannan wata kyakkyawar dama ce ta yin kasuwanci. Mun yi amfani da wannan dama mun bullo da sabon samfurin motarmu."

Lokacin da wakilinmu yake neman labaru a kasuwannin mota, ya gano cewa, kamfanonin kera motoci na kasar Sin sun habaka tsarin ba da hidimar gyara mota a kauyuka domin sanya motocinsu su yi suna kuma su samu karin kaso a kasuwa. Sakamakon haka, manoma za su iya samun sauki wajen gyara motocinsu. Mr. Yang Jie, babban direktan kamfanin sayar da motoci na kamfanin General-Mitsubishi na Shanghai ya bayyana cewa, tsarin ba da hidimar gyara mota na kamfaninsu ya shafi wurare da yawa. Ko shakka babu wadannan tasoshin ba da hidima za su iya biyan bukatun da manoma suke da su. Mr. Yang ya ce, "Mun riga mun kakkafa garejin gyara motoci a matsakaitan biranen da yawansu ya kai kashi 90 cikin kashi dari bisa na dukkan matsakaitan biranen kasar Sin. Sannan, yawan garuruwan da ke matsayin gunduma da muka kakkafa garejin gyara motoci ya kai fiye da kashi 30 cikin kashi dari. Alal misali, a wasu yankuna masu arziki, kamar su lardunan Jiangsu da Shandong, mun riga mun kafa tasoshin gyara motoci a dukkan gundumominsu gaba daya. Bisa wannan kokarin da muka yi, ba ma kawai yawan motocin da muke sayarwa ya samu karuwa cikin sauri ba, har ma masu sayen motocinmu sun samu sauki wajen gyara motocinsu."

Kasar Sin ta kasance tamkar kasa mafi girma ta biyu wajen mallakar motoci, an yi hasashen cewa, yawan motocin da za a sayar da su a kasar Sin zai kai fiye da miliyan 10 a shekarar da ake ciki. Sannan, wasu hukumomin gwamnatin sun yi hasashen cewa, bayan da aka aiwatar da manufofin samar da motocin da suke dacewa da muhallin kauyuka, yawan motocin da za a sayar da su a kauyukan kasar Sin zai wuce miliyan 1 a bana. (Sanusi Chen)


1 2 3