Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-15 17:00:50    
Kasuwar sayar da motoci a kauyuka ta samu ci gaba cikin sauri

cri

Da misalin karfe 6 na sassafe, Yang Yuangcheng wanda yake zaune a kauyen Mei na birnin Weifang na lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin ya tashi motarsa kan lokaci, kuma ya tuka wannan motar daukar kaya zuwa wata kasuwar da ke cikin birnin Wenfang domin sayen kaya don sama a wani karamin kantin da ya kafa da kansa a kauyen. Tun cikin watan Maris na shekarar da ake ciki, wannan ya riga ya zama wani abun da tilas ne Yang Yuancheng ya yi a kowace rana. Kafin watan Maris na shekarar da ake ciki, sayen wata mota da kansa fata ne da ya dade yana cikin zuciyarsa. Mr. Yang Yuancheng ya ce, "Na kan sayi kayayyaki a kasuwar da ke cikin gari. Amma sabo da yawan kayayyakin da nake saya suna da yawa, dole ne na yi hayar wata mota domin sufurin kayayyakin da na saya. Idan ina da wata mota, zai fi mini sauki. A waje daya, zan iya yin amfani da wannan mota domin sufurin kayayyaki, kuma zan iya samun karin kudi."

A hakika dai, mallakar wata mota kamar yadda mazauna birane suke yi ya riga ya zama wani fata na dimbin manoman da suka samu arziki. A lokacin da aka sheda illa ga kasuwar cinikin motoci a birane a sanadiyyar rikicin kudi na duniya, gwamnatin kasar Sin ta zura ido kan kasuwannin kauyuka. Sabo da haka, hukumomin gwamnatin kasar sun bullo da jerin manufofi masu gatanci domin sa kaimi ga masana'antu da kamfanonin harhada motoci da su sayar da motoci a kauyuka, kuma sun sa kaimi ga manoma su sayi kananan motoci da motocin daukar kaya da suke dacewa da muhallin kauyuka. Bisa manufofin da gwamnatin kasar Sin ta bullo da su, yawan tallafin kudin da manomin da ya sayi mota zai samu za su kai kudin Sin yuan dubu 5. Wannan manufa ta sanya manoma suna son sayen mota.

1 2 3