Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-15 17:00:50    
Kasuwar sayar da motoci a kauyuka ta samu ci gaba cikin sauri

cri

Bayan da aka aiwatar da manufar, Yang Yuancheng ya tsai da kudurin sayen wata karamar motar da kamfanin General-Mitsubishi na Shanghai na kasar Sin ya kera da farashinta ya kai kimanin kudin Sin yuan dubu 30 kawai, wato kimanin Naira dubu dari 6. Ya gaya wa wakilinmu cewa, "Yawan harajin da aka rage ya kai kudin Sin yuan dubu 2, sannan, bisa shirin da gwamnatin kasar ta bayar, za a mayar mini kudin da ya kai kashi 10 cikin dari bisa na jimillar kudin wannan mota, wato zan iya yin tsimin kudin Sin kimanin yuan dubu 3. Sabo da haka, idan na sayi wannan mota, zan iya yin tsimin kudin Sin yuan dubu 5, wato idan na sayi wata motar da farashinta ya kai kimanin kudin Sin yuan dubu 30, zan biya kudin Sin yuan dubu 20 da wani abu ne kadai."

A da, sabo da manoma ba su da fatan sayen mota, yawan motocin da aka sayar a kauyukan ya yi kadan. Galibin kamfanonin kera motoci ba su mai da hankali kan kasuwannin mota na kauyuka ba, kuma su kan mai da hankali a kasuwannin mota na birane kawai. Amma bayan da aka soma aiwatar da manufar sayar da mota a kauyuka, wasu kamfanonin kera motoci sun gano damar kasuwanci a kauyuka, kuma bi da bi ne suka soma kera motocin da suke dacewa da muhallin kauyuka. Kamfanin General-Mitsubishi na babban kamfanin motoci na Shanghai yana daya daga cikinsu. Mr. Yang Jie, babban direktan kamfanin sayar da mota na kamfanin General-Mitsubishi na Shanghai ya bayyana cewa, ya kasance tamkar kamfanin mota mafi girma wajen mallakar kasuwar kananan motoci a kauyuka na kasar Sin yanzu, kamfanin General-Mitsubishi na Shanghai ya samu moriya sosai daga manufar samar da motoci ga kauyuka. Yawan motocin da a kan sayar ya karu cikin sauri. Mr. Yang ya ce, "A farkon watanni 3 na shekarar da ake ciki, yawan motocin da muka sayar ya riga ya kai dubu 240, wato ya karu fiye da kashi 32 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Har yanzu ana sayar da kananan motocinmu a kauyuka cikin sauri. Sabo da haka, muna murna sosai."

A hakika dai, ba kamfanonin harhada motoci kawai suke murna ba, har ma 'yan kasuwa wadanda suke sayar da motoci suna murna kwarai da gaske. A cikin kantin sayar da motoci kirar Chang'an da ke karkarar arewacin birnin Beijing, mutane da yawa suna duba motoci a kowane karshen mako. Mr. Li wanda ke kula da wannan kanti ya gaya wa wakilinmu cewa, "Bisa goyon baya na manufar, yanzu kamfanonin kera motoci ba su da isassun motocin da za a iya sayar da su. Yanzu mu kan yi odar motocin da ake bukata a farkon kowane wata. Sakamakon haka, yawan motocin da ake ajiyewa a kantinmu ya kai kimanin 100 a kowane wata domin tabbatar da ganin manoma sun iya sayen motocin da suke bukata kan lokaci."

1 2 3