Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-03 16:04:20    
Bayani kan taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Sahel da Sahara ta Afrika

cri

Taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Sahel da Sahara da aka yi a wannan gami ya daidaita matsayin kasashen kungiyar kan kafa gwamnatin hadin kan Afrika da canza sunan kwamitin tarayyar Afrika?wato hukumar dindindin ta tarayyar Afrika zuwa hukumar iko ta tarayyar Afrika. Shugabanni mahalartan taron sun yi kira a tabbatar da kudurin da aka tsayar a taron kolin tarayyar Afrika a karo na 12 na canja sunan kwamitin tarayyar Afrika zuwa hukumar Tarayyar Afrika kan lokaci.taron ya yi kira ga kasashen kungiyar tarayyar Sahel da Sahara da su shiga kokarin da ake yi na kawo sauyi ga hukumar kwamitin tarayyar Afrika da samu matsayi bai daya cikin sauri. An kafa kungiyar tarayyar Sahel da Sahara ne a shekara ta 1998 wadda take da mambobin kasashe 28 da yawansu ya zarce rabin kasashen kungiyar tarayyar Afrika,wadda ta fi girma daga kungiyoyin tarayya na tattalin arziki a nahiyar Afrika,kuma tana da kashi 45 bisa dari na fadin Afrika da rabin mutanen Afrika baki daya,ana kiranta tushen kungiyar tarayyar Afrika.hedkwatar kungiyar yana Tripoli,babban birni na kasar Libya,an kafa kungiyar ne tare da nufin karfafa hadin kan kasashen kungiyar ta fuskar siyasa da tattalin arziki da kuma kiyaye tsaron yanki da hadin kan yankin.

Bisa muhimmin matsayi na kungiyar tarayyar Sahel da Sahara a kungiyar Tarayyar Afrika,ana iya kyautata zaton cewa kungiyar tarayyar Sahel da Sahara za ta taka rawara zo a gani a taron koli na tarayyar Afrika da za a yi a farkon watan Yuli da muhimman batutuwa na Afrika a nan gaba. Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na Afrika a yau. Mun gode muku saboda kun saurarenmu.(Ali)


1 2 3