Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-03 16:04:20    
Bayani kan taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Sahel da Sahara ta Afrika

cri

A cikin jawabinsa na fatan alheri,shugaban kungiyar tarayyar Afrika a yanzu kuma shugaban kasar Libya Gaddafi ya bukaci kungiyar tarayyar Sahel da Sahara da ta kafa wata tawaga da wakilan kasashen Sudan da Chadi za su halarta don tsara wani shirin filla filla kan warware matsalar da aka samu game da dangantaka dake tsakaninsu. Ya kuma yi kira ga shugaban kasar Sudan Bashir da takwaransa na Chadi Debi da su kula da jama'ar kasashensu da Afrika,ya kuma yi kashedi cewa ba zai yi watsi da karfin soja da sanya takunkumi ba wajen kawar da rikicin dake tsakanin Sudan da Chadi.Kudurin bayan taron ya bukaci shugabanni na kasashen nan biyu da su ba da dama ga shugaba Gaddafi wajen shiga tsakani. Halin da ake ciki a kasar Somaliya na ci gaba dasheda cikas,a kan kuma samun tashe tashen hankula da dama a wannan kasa,shugabannin dake halartar taron sun nuna damuwarsu a kai. Sun nuna bakin cikinsu ga kin shiga tattaunawa da kungiyar dakaru masu adawa da gwamnati ta yi da hana a kafa gwamnatin wucin gadi ta tarayya da gudanar da ayyukan da sojojin hadin gwiwar tabbatar da zaman lafiya na Afrika suke yi,sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasar Somaliya Ahmed da fatansa da gwamnatin wucin gadi da majalisar dokoki ta wucin gadi su ci gaba da kokarinsu na maido zaman oda da kwanciyar hankali a wannan kasa. Za a kira taron koli na kungiyar tarayyar Afrika a karo na 13 a farkon watan Yuli a kasar Libya.

1 2 3