Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-03 16:04:20    
Bayani kan taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Sahel da Sahara ta Afrika

cri

Taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Sahel da Sahara ya yi kira ga Afrika da ta kawo karshen yake yake da samun hadin kai tsakaninsu. Assalamu alaikum jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a wannan lokaci na shirin Afrika a yau.A cikin wannan shirin namu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya rubuta kan wani taron koli na kungiyar tarayyar Sahel da Sahara.

A ran 30 ga watan jiya da dare an kammala taron koli na yini biyu na kungiyar tarayyar Sahel da Sahara a karo na 11 a kasar Libya. Shugabanni dake halartar taron sun yi kira ga kasashen Afrika da su kawo karshen yake yake cikin sauri da tabbatar da hadin kan Afrika. Kasashen manbobi 28 na kungiyar nan sun halarci taron ciki har da shugabannin kasashe goma.An tattauna batutuwa da dama da zartas da kudurai da yawa,muhimman fannoni biyu da aka fi mayar da hankali a kai su ne da farko ta yayya za a kawar da bambancin ra'ayi da rikici a tsakanin kasashen wannan kungiyar,na biyu kasashen kungiyar su nuna daidaito ta yadda za su dauki matsaya daya a taron koli na kungiyar tarayyar Afrika da za a kira nan gaba kadan. Kasashen Sudan da Chadi suna yaki da juna a tsawon shekaru da dama da yake sun taba daddale yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu bayan da aka shiga tsakani har wa yau dai dangantakar dake tsakaninsu tana cikin sarkakiya.Ko ma a taron da aka yi bangarori biyu ba su samun ci gaba ba kan sassauta rikicin da ke tsakaninsu.Shugaban kasar Sudan da na Chadi sun bar taron sun koma gida bayan da suka halarci bikin bude taron kawai. Sabili da haka taron kolin ya nuna rashin jin dadii kan dangantakar dake tsakanin kasashen nan biyu da ta ci gaba da yin muni.

1 2 3