Yanzu, ana zaton ko wannan shirin farfado da kamfanin General zai sanya sabon kamfanin General ya samu farfadowa? Wannan ya zama wata tambayar da ke jawo hankalin mutane. Manazarta suna ganin cewa, bisa matsayi da manufofin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka, ana da fatan samun nasarar aiwatar da wannan shiri. A ran 27 ga watan Afrilu, bayan da kamfanin General ya bullo da shirin sanya bashin ya zama takardun hannun jari, wato wadanda suke mallakar ikon basusukan da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 27 za su iya mayar da bashin da yazama takardun hannun jarin da yawansu ya kai kashi 10 cikin kashi dari bisa na jimillar yawan takardun hannun jari na sabon kamfanin General, amma masu bin bashin sun ki amincewa da wannan shiri. Sakamakon haka, gwamnatin kasar Amurka ta samu tudun dafawa, ta bayar wa masu mallakar bashi ikon sayen takardun hannun jari da yawansu ya kai kashi 15 cikin kashi dari na sabon kamfanin General motors.
Dadin dadawa, bayan da gwamnatin Amurka ta zuba rancen kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 19.4 domin yakar rikicin, ta sake kebe dalar Amurka biliyan 30 daga aljihunta ga sabon kamfanin General. Wannan wani sabon gwaji ne da ba a taba yi ba a tarihin sana'o'in kasar Amurka, ko gwamnati ko majalisun dokoki na kasar Amurka dukkansu suna son kiyaye kamfanin General wanda ke wakiltar masana'antun kasar Amurka.
1 2 3
|