Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 16:01:43    
Ko kamfanin General motors na kasar Amurka zai samu farfadowa?

cri

Bayan da jerin shirye-shiryen sake bunkasa kamfanin kera motoci na General motors na kasar Amurka suka ci tura, kamfani wanda shi ne kamfanin kera motoci mafi girma a kasar Amurka ya kama hanyar kusan rufe kofar ayyukansa. A ran 1 ga wata, kamfanin General motors ya gabatar da takardar neman kariya ga wata kotun tarayyar Amurka da ke shiyyar kudu ta New York. Sabo da haka, ya zama batun neman rufe kofa mafi girma a tarihin sana'ar kira ta kasar Amurka. Bisa shirin farfado da kamfanin mota na General da gwamnatin kasar Amurka ta tsara, gwamnatin Obama za ta sanya kamfanin mota na General ya zama wani kamfanin gwamnati cikin dan lokaci domin tabbatar da ganin kamfanin ya haye wannan mawuyacin hali. Ko wannan shiri zai iya sanya kamfanin mota na General ya samu farfadowa, ya zama wani batun da ya fi jawo hankalin mutane.

Bisa wannan shirin da gwamnatin kasar Amurka ta tsara, kamfanin mota na General zai sayar da kyawawan kadarorinsa ga sabon kamfanin General motors da za a kafa, sannan gwamnatin Amurka za ta samar da dalar Amurka biliyan 30 ga wannan sabon kamfani domin tabbatar da ganin ya aiwatar da harkokinsa kamar yadda ake fata. A cikin wannan sabon kamfanin General motors, gwamnatin Amurka za ta mallaki takardun hannun jari da yawansu ya kai 60 cikin kashi dari, wato za ta zama mai hannun jari da ke mallakar ikon mulkin sabon kamfanin General motors. Sannan gwamnatin kasar Canada za ta mallaki takardun hannun jari da yawansu ya kai kashi 12.5 cikin kashi dari, kungiyar 'yan kwadagon sana'ar motoci za ta mallaki 17.5%. Bugu da kari kuma, wadanda suka samar wa tsohon kamfanin General rancen kudi za su mallaki kashi 10% a cikin sabon kamfanin General motors. Za a kammala aikin daidaita tsarin hannun jari cikin kwanaki 60 zuwa kwanaki 90 masu zuwa. A cikin wannan lokaci, yawan 'yan kwadago da kamfanin General zai sallama zai kai dubu 21 a kasar Amurka, sannan kamfanin General zai rage rabin tamburorinsa a kasuwar cikin gida ta Amurka. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, sabon kamfanin General zai bar kason da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 79.

1 2 3