Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 11:13:19    
Bikin wasan kwallon kafa na yara maza da shekarunsu ba su kai 13 ba da kungiyar AFC ta shirya a shekarar 2009

cri

George Cumming, wani mashawarci ne na sashen horar da alkalan wasanni, kuma dan kasar Scotland ya halarci wannan bikin wasan kwallon kafa da aka yi a Xianghe tun daga farko har zuwa karshe. A matsayinsa na wani mashawarci a fannin horar da alkalan wasanni matasa, ya yi karin bayani kan aikin horaswa a yayin bikin. Yana mai cewar,"Alkalan wasanni matasa 18 da suka zo daga kasashen Sin da Korea ta Kudu da Japan da sauran mambobi 6 na kungiyar AFC sun samu aikin horaswa kafin bikin. Daga baya sun aiwatar da ka'idojin gasa a cikin gasanni a yayin bikin. Bisa matsayinsu na aiwatar da ka'idojin gasa, mun zabi wadanda suka fi yin fice. A watan Nuwamba na wannan shekara, su da takwarorinsu daga bukukuwan wasan kwallon kafa na sauran yankuna 5 na Asiya za su halarci wata jarrabawa. A wannan lokaci za mu zabi wadanda suka fi yin fice daga wajensu, daga baya, wadanda suka fi yin fice za su shiga aikin horaswa na tsawon shekaru 2 da kungiyar AFC ta shirya. Za su zama ginshikai a tsakanin alkalan wasanni na Asiya."

Mr. Cumming ya ci gaba da cewa, Asiya mai yawan mutane biliyan 3.7 na matsayin makoma ce a fannin raya wasan kwallon kafa na duniya. A sakamakon shirya bikin wasan kwallon kafa da kuma gudanar da shirin 'Vision Asia', wasan kwallon kafa na Asiya zai samu bunkasuwa, haka kuma, malaman horas da wasanni da alkalan wasanni za su kyautata karfinsu sosai. Ya yi imani da cewa, nan gaba ba da dadewa ba, kungiyar wasan kwallon kafa ta wata kasar Asiya za ta ci kofin duniya wato World Cup.(Tasallah)


1 2 3