Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 11:13:19    
Bikin wasan kwallon kafa na yara maza da shekarunsu ba su kai 13 ba da kungiyar AFC ta shirya a shekarar 2009

cri

Kalmomin Qi Hong sun tono mana ainihin burin kungiyar AFC na shirya bikin wasan kwallon kafa. Wannan bikin wasan kwallon kafa ya sha bamban sosai da gasannin da muka saba gani a kullum. Baya ga tsawon lokacin gasa, filin wasa da kwallon kafa da aka yi amfani da su a yayin bikin suna da kankanta bisa wadanda aka saba yin amfani da su a kullum. Sa'an nan kuma, alkalan wasanni ba kawai sun iya nuna wa 'yan wasa kati mai launin ja da rawaya domin nuna musu gargadi ba, har ma sun iya nuna wa wasu 'yan wasa kati mai launin kore. Zhu Heyuan, darektan sashen harkokin samari da yara na kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ya yi mana karin bayani da cewa,"Dalilin da ya sa alkalan wasanni suka nuna wa wasu 'yan wasa kati mai launin kore shi ne domin karfafa gwiwarsu dan su nuna kyakkyawar da'a a filin wasa. Alal misali, a lokacin gasa, ka kayar da wani abokin karawa, amma ka daga shi don karan kanka. Ana karfafa gwiwar 'yan wasa su yi haka. Dan haka an shirya wannan bikin wasan kwallon kafa ne da zummar horar da yara su samu madaidaiciyar fahimta kan wasan kwallon kafa da kuma nuna kyakkyawar da'a a filin wasa."

A gaskiya, gasa wani bangare ne kawai na wannan bikin wasan kwallon kafa. Annathurai Ranganathan, wani jami'in sashen harkokin samari da yara na kungiyar AFC ya yi bayani da cewa,"A yayin bikin na tsawon makwanni 2, an shirya kwasa-kwasan horas da malaman horas da wasanni matasa da alkalan wasanni matasa da gasa a tsakanin kungiyoyin 'yan wasan da shekarunsu ba su kai 13 da haihuwa ba da sauran harkoki 3. A sakamakon shugabancin wasan kwallon kafa na Asiya, kungiyarmu ta AFC mun gano muhimancin kyautata karfin 'yan wasan kwallon kafa yara. Bikin wasan kwallon kafa da kungiyar AFC ta shirya yana nuna wa samari su bi madaidaiciyar hanya."

Domin yin tsimin lokacin gasanni da kuma kudaden shirya gasanni, kungiyar AFC ta kan shirya wa yaran da shekarunsu ba su kai 13 da haihuwa ba bikin wasan kwallon kafa a ko wace shekara a yankunan gabashin Asiya da tsakiyar Asiya da kudancin Asiya da kudu maso gabashin Asiya da kuma yammacin Asiya daya bayan daya. Wannan biki wani muhimmin bangare ne na shirin 'Vision Asia' da kungiyar AFC ta kaddamar da shi daga shekarar 2003 domin yin amfani da zaratan gobe ne 'yan Asiya na yin wasa da kwallon kafa, ta haka za a iya daga matsayin duk Asiya ta fuskar wasan kwallon kafa.

Shirin 'Vision Asia' ya hada da bangarori 11, wato raya wasan kwallon kafa na yara da horar da malaman horas da wasanni da alkalan wasanni da ba da magani ga 'yan wasa da bunkasa kasuwanni da sauran fannoni 6. Kungiyar AFC ta kuma gayyaci mashawarta da dama daga duk fadin duniya domin gudanar da wadannan bangarori 11 yadda ya kamata.

1 2 3