Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 11:13:19    
Bikin wasan kwallon kafa na yara maza da shekarunsu ba su kai 13 ba da kungiyar AFC ta shirya a shekarar 2009

cri

Masu karatu, barka da war haka! Shirin nan da kuke saurara a yanzu shirinmu ne mai farin jini da mu kan gabatar da shi a ko wace ranar Laraba dangane da wasannin motsa jiki. Ni Tasallah ce ke farin cikin sake saduwa da ku a wannan shiri.

A kwanan baya, an rufe bikin wasan kwallon kafa na yara maza da shekarunsu ba su kai 13 da haihuwa ba da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya wato AFC ta shirya a shekarar 2009 a sansanin horar da 'yan wasan kwallon kafa na kasar Sin a gundumar Xianghe da ke arewacin kasar Sin. A matsayin muhimmin bangare na shirin "Vision Asia" da ta tsara domin raya wasan kwallon kafa a Asiya, kungiyar AFC tana fatan wannan bikin wasan kwallon kafa za ta sa kaimi kan bunkasuwar wasan kwallon kafa a tsakanin jama'a da kuma samari.

A 'yan kwanakin da suka wuce, an rufe bikin wasan kwallon kafa na yara maza da shekarunsu ba su kai 13 da haihuwa ba da kungiyar AFC ta shirya a shekarar 2009 a sansanin horar da 'yan wasan kwallon kafa na kasar Sin a gundumar Xianghe. Wannan biki ya samar wa yara wata kyakkyawar damar jin dadin yin wasa da kwallon kafa da motsa jiki da kuma inganta zumunci a tsakaninsu. Domin bai wa duk yaron da ya halarci bikin wani zarafin shiga gasanni, kungiyar AFC ta kafa ka'idojin cewa, tsawon lokacin ko wace gasa bai wuce mintoci 30 ba, kuma ta raba kungiyoyi zuwa bangarori 2, wadanda ko wanensa ke da mambobi 11, dukkan bangarorin 2 sun iya shiga gasa. Ko da yake ko wace kungiya ta rabu ne zuwa bangarori 2, amma kungiyar wasan kwallon kafa ta yara ta kasar Sin ta yi fice sosai, sun lashe kungiyoyin kasashen Korea ta Arewa da Korea ta Kudu da sauran kungiyoyin kasashen Asiya masu karfi a wannan karo, kuma bangarenta na A bai sha kaye ba a cikin dukkan gasanni 7 da ya shiga, ya kasance kan gaba. Duk da haka, Qi Hong, babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta shiga wannan gasa ne domin sanya yara su ji dadin yin wasa da kwallon kafa, a maimakon samun maki mai kyau. Inda ya ce,"Su yara ne kawai. Muna fatan za su iya jin dadin samun aikin horaswa da shiga gasanni da kuma zaman rayuwa. Ba mu bukace su su tashi haikan dan samun maki mai kyau ba. Bayan da muka isa Xianghe, na gaya wa mambobin kungiyata jin dadin shiga gasanni da kuma dawowa gida cikin farin ciki. Ina fatan dukkansu za su iya samun sabbin abokai a nan tare kuma da nuna gwanintarsu ta fuskar wasan kwallon kafa a yayin wannan biki."

1 2 3