
A kwanakin baya, al'amuran fashin da 'yan fashin teku na kasar Somali suka yi wa jiragen ruwan 'yan kasuwa sun sake karuwa, Mr. Meng Xiangqing yana ganin cewa, "Al'amuran fashi sun sake karuwa a kwanakin baya, wannan kamar martani ne da aka mayar kan matakan da kasashen duniya suka dauka. Idan an kai farmaki gare su, za a sami sakamako biyu, da farko shi ne, za a lalata su sosai. Na biyu shi ne za su mai da martani mai zafi. Ban da haka kuma, ko da yake wasu kasashe sun aika da jiragen ruwan yaki zuwa tekun kasar Somali domin ba da kariya ga jiragen ruwan da ke tafiya kan wannan yanki, amma sansanin 'yan fashin teku yana cikin kasar Somali, saboda haka, kai farmaki ga 'yan fashi kan teku ba zai warware wannan matsala daga tushe ba."
1 2 3
|