Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-07 16:50:00    
Bayani kan matsalar 'yan fashi a tekun Somali

cri

A cikin shekaru daya da ya wuce, matsalar 'yan fashi a teku da ke kasar Somali ta yi tsanani, ko da yake kasashen duniya sun dauki matakai daban daban, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya zartar da wani kudurin da abin ya shafa, kuma wasu kasashe sun aika da jiragen ruwan soja zuwa mashigin tekun Aden da tekun kasar Somali domin kiyaye jiragen ruwan ciniki na kasashe daban daban da ke wucewa wannan yanki, har ma an dauki matakai domin kai farmaki ga 'yan fashi da kama su. Amma 'yan fashi suna ci gaba da garkuwa da jiragen ruwan ciniki a kwanakin baya. Game da wannan matsala, wakilinmu ya yi hira da Shehu malami Meng Xiangqing na kwalejin ilmin huldodin tsakanin kasa da kasa na jami'ar tsaro ta kasar Sin.

Mr. Meng Xiangqing yana mai ra'ayi cewa, karfin soja ba zai iya warware matsalar 'yan fashi a teku na kasar Somali ba. Ya ce, "An sami matsalar 'yan fashi a teku tun daga shekarar 2000, yan fashi suna ta karuwa cikin shekaru 10 da suka wuce. Kuma mashigin tekun Aden shi ne muhimmiyar hanyar da ke hada tekun India da tekun Maliya, an kira shi hanyar ruwa mai zinariya, jiragen ruwan 'yan kasuwa da yawa suna tafiya kan wannan hanya. Tun daga shekaru 90 na karni na 20, kasar Somali take yakin basasa da kuma kasancewa cikin halin rashin samun tsayayyar gwamnati, mutanen kasar suna zama cikin mawuyacin hali. Sakamakon haka, wasu talakawa sun fara yi fashi kan teku, daga baya sojoji sun fara wannan laifi. A ganinmu su 'yan fashi ne, amma a ganinsu su kungiyar tsaron teku ne. Wato a ganinsu, wannan yankin teku nasu ne, idan jiragen ruwa suna tafiya kan wannan hanya, dole ne su biya kudi. Sabo da haka, muna masu ra'ayi cewa, karfin soja yana da amfani wajen shawo kan wannan matsala, amma ba za a iya warware wannan matsala daga tushe ba."

1 2 3