Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-06 17:22:50    
Kenya na kokarin sayar da ganyen shayi zuwa kasashen waje

cri

Bisa alkaluman da hukuma mai kula da abinci da aikin gona ta MDD ta bayyana, a shekarar 2008, yawan ganyen shayi da aka samar bai kai yawan ganyen da ake sha ba, hakan ya sa farashin ganyen shayi a kasuwannin duniya na dinga hauhawa. Sa'an nan ganyen shayi na ti daga kasar Kenya na samun karbuwa sosai a duniya, musamman ma ganyen irin 'yan kanana, wanda ya sa Mombasa, birnin Kenya da ke bakin teku, ya zama wata cibiyar da ake saye da sayar da ganyen shayi na duk kasashen gabashin Afirka. Haka kuma, duk da cewa, an samu fari da fadi-tashi kan halin siyasa a kasar Kenya, amma ba su yi illa ga aikin samar da ganyen shayi sosai ba. Hakan ya sa kasar ta samu kudin shiga na shilling biliyan 62.1 a shekarar 2008, bisa fitar da ganyen shayi zuwa kasashen waje, haka kuma jimillar ta karu da kashi 44% idan an kwatanta da yawan fitar da ganyen shayi na shekarar 2007. Sa'an nan a halin da ake ciki, farashin ganyen shayi ya haura zuwa dalar Amurka 3 ko wane kilo daga dala 2.3 ko wane kilo na shekarar 2008, abun ya karfafa wa gwamnatin kasar Kenya gwiwa sosai. Da ma, kasar Kenya ta kan sayar da ganyen shayi zuwa kasahen Masar, da Pakistan, da kuma Birtaniyya. Sai dai bisa halin da ake ciki na fama da rikicin hada-hdar kudi da rashin zaman karko a kasuwannin duniya, ma'aitakar aikin gona ta kasar Kenya ta ba da shawarar kara sayar da ganyen shayi zuwa gabashin Asiya da gabashin Turai, domin tattalin arzikin gabashin Asiya na ci gaba da karuwa, kuma kasashen gabashin Turai za su rage harajin kwastam da ake karbuwa bayan da suka shiga cikin kungiyar EU.(Bello Wang)


1 2 3