Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-06 17:22:50    
Kenya na kokarin sayar da ganyen shayi zuwa kasashen waje

cri

Cikin shirin yau za mu duba halin da ake ciki a kasar Kenya kan kokarin da ake yi don sayar da ganyen shayi zuwa kasashen waje. An ce, kasar Kenya na yawan samar da ganyen shayi, wanda har ma yawansa ya kai kashi 10% cikin dukkan ganyen shayi da ake samu a duniya. Sa'an nan kasar Kenya, bisa matsayinta na kasar da ta fi yawan samar da ganyen shayi da sayar da su zuwa kasashen waje a nahiyar Afirka, tana cikin kasashe 3 da suka fi yawan fitar da ganyen shayi zuwa kasashen duniya. Sai dai a halin yanzu, yayin da take fama da matsalar karancin abinci, kasar Kenya na kokarin bunkasa aikinta na sayar da ganyen shayi zuwa kasuwannin duniya, ta yadda za ta iya cin gajiyar hauhawar farashin ganyen shayi, da samun isasshen kudi don sayo abinci daga kasashen waje.

Da ma aikin gona ya kasance daya daga cikin manyan ayyuka na kasar Kenya wadanda gwamnatin kasar ke dogaro kansu don samun kudin shiga. Amma, tun daga rabin shekara na karshe na shekarar bara, fari ne ya sa kasar Kenya sannu a hankali ta fada cikin mawuyacin hali na karancin abinci. Zuwa farkon shekarar bana, gwamnatin kasar Kenya ta sanar da dokar ta-baci kan halin rashin abinci, inda aka samu mutane miliyan 10 daga cikin daukacin jama'ar kasar Kenya miliyan 35 wadanda ke fuskantar yunwa.

1 2 3