Sa'anan kuma, Mr Feng Yuanzhen ya nuna wasanni da yawa dangane soyayya a cikin gida , alal misali, wasan da ke da lakabi haka: "Soyayya ta shiga tsakaninsu, sa'anan kuma an yi watsi da ita, abubuwan da ya nuna a cikin wasan an bayyana wani namijin da ba ya iya kwantawa da matarsa, abubuwan da ya nuna sun bayyana wahalhalu da sabanin da wannan namijin ya ji a cikin zuciyarsa sosai da sosai, saboda haka a ganin wasu 'yan kallo, Feng Yuanzheng shi ne wanda ya saba da halin da sauran mutane suke yi a yau da kullum, kuma shi ne mai nuna karfin tuwo a cikin gida. Game da wannan, Mr Feng Yaunzheng ya ji cewa, babu sauran zabi na daban gare shi. Ya bayyana cewa, kwanan nan, mutane suna kan cewa, kai ne kwararre mai nuna wasanni kan mazan da suke da matsaloli da yawa, amma na gaya musu cewa, babu wani zabi a gare shi, wannan dangane da ra'ayoyin da mutanen kasar Sin suke da su a kan soyayya ne. A cikin wasannin da aka yi, idan an kori wata macen daga gidan mijinta bisa sakamakon da ta kaurar da soyayyarta zuwa ga wani namiji, mai yiyuwa ne 'yan kallo ba za su iya amince da wannan ba. Sai ake mayar da laifin nan ga mijinta.
Daya ke abubuwan da Feng Yuanzheng ya nuna a dandalin wasa sun shiga zuciyar mutane sosai, sai wasu 'yan kallo suka amince cewa, shi ne namijin da ke da matsaloli da yawa a cikin zaman rayuwarsa na yau da kullum. Kwanan baya ba da dadewa ba, Feng Yaunzheng da matarsa Liang Danni sun rubuta wani littafi cikin hadin guiwa, a cikin littafin, sun rubuta wasu abubuwa da wahalhalun da suka sha a cikin zaman aurensu a shekaru 15 da suka wuce . Littafin ya gaskanta abubuwan da wasu 'yan kallo suka yi shakka gare su dangane da soyayyarsu. Feng Yaunzheng ya bayyana cewa, da ni da matata Liang Danni dukkanmu muna da hanyoyin da muke bi wajen zaman rayuwarmu. Da farko, ya kamata mu mai da hankali ga tunaninmu wajen zaman aurenmu, a littafin, mun rubuta yadda ni kaina da matata Liang Danni dukkanmu muka samar wa juna wani sarari . In tsawon lokacin aurenmu ya kai shekaru 10 ko 15 ko 20, a hakika dai ne, dangantakarmu wajen zaman aure tana sauyawa, dangantakarmu ta aure ta riga ta zama irin dangantakar da ke tsakanin dangogi, amma irin wannan sauyawa ita ma ta zama soyayya gare mu.
Kwanan nan, a gidan televition na birnin Beijing, an nuna film ta Telebijin mai suna "wani dan sarki na karshe". Sinimar ta bayyana cewa, daga lokacin da aka tunbuki daular Qing ta karshe ta kasar Sin har zuwa lokacin da aka kafa sabuwar kasar Sin, wato Jamhuriyar jama'ar Sin a shekarar 1949, wani dan sarki na karshe na kasar Sin mai suna Shou Yuan ya zama farar hula daga mai hannu da shuni na gidan sarauta. Feng Yaunzheng ya zama babban dan wasan, wato ya nuna wasa dangane da dan sarkin, kuma matarsa Liang Danni ta nuna wasa dangane da mahaifiyar dan sarkin. Abubuwan da suka nuna a cikin wasan sun samar wa 'yan kallo abubuwan da suka yi cikin hadin guiwa sosai.
Mr Feng Yuanzheng ya bayyana cewa, ga ni ina samun alheri sosai, abun da ya fi ba ni alheri shi ne dandalin nuna wasanni na gidan nuna fasahohin jama'a na birnin Beijing, 'yan wasa da yawa suna son samun damar shiga gidan nan.
Feng Yaunzheng ya ci gaba da cewa, babu iyakar da zan yi koyon fasahar wasanni , ina bukatar ci gaba da koyon fasahohin da aka samu, idan ban yi haka, to tabbas ne zan rasa 'yan kallon da ke kaunata . To, jama'a masu sauraro, mun dai karanto muku bayanin da ke da lakabi haka: wani mashahurin dan wasa na kasar Sin mai suna Feng Yuanzheng. To da wannan muka kawo muku karshen shirinmu na yau na al'adun kasar Sin. Halima ce ta shirya ta karanto muku, sa'anna kuma take cewa, assalamu alaikum! (Halima) 1 2 3
|