Feng Yuanzheng yana daya daga cikin 'yan wasan da 'yan kallon kasar Sin suke kaunarsu sosai. A cikin shekaru da yawa, sifofin mutanen da ya nuna a cikin wasannin kwaikwayo sun shiga cikin tunanin mutane sosai a yayin da wasu 'yan kallo suka mayar da shi bisa matsayin mutanen da ya sifanta a cikin wasannin kwaikwayo, kuma a cikin zaman rayuwarsa na yau da kullum, ya kan gamu da wasu abubuwa rashin jin daji.
Shekarun haihuwa na Feng Yuanzheng sun kai 46. A lokacin da ya cika shekaru 23 da haihuwa , ya sami aiki a gidan nuna fasahohin jama'a na birnin Beijing ta hanyar jarrabawar da aka yi masa. A shekarar 1989, bisa gayyatar da aka yi masa, ya yi dalibta a babbar kwalejin koyar da fasahohi ta Berlin na kasar Jamus don koyon ilmin nuna wasannin kwaikwayo. A shekarar 1991, ya koma gidansa, yanzu ya zama dan wasa na gidan nuna fasahohin jama'a na birnin Beijing. Ya zuwa yanzu, ya nuna wasanni a cikin sinima da kafofin Televition da yawansu ya wuce goma, 'yan kallo sun dauke shi bisa matsayin dan wasan da ke da hakikanin kwarewa wajen nuna wasanni. Yawancin mata masu ilmi suna kaunarsa sosai da sosai, kuma suna son kallon wasannin da ya nuna. Sa'anan kuma, an mayar da shi bisa matsayin wakilin maza masu ilmi.
Amma a shekarar 2002, Feng Yuanzheng ya gamu da matsaloli da yawa sakamakon nuna wasan kwaikwayo ta cikin kafar televition wanda ke da lakabi haka: kada ka yi magana da wanda ba ka san shi sosai ba.
1 2 3
|