Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-06 16:08:48    
Wani mashahurin dan wasa na kasar Sin mai suna Feng Yaunzheng

cri

A wani kashi da ke cikin wasan kwaikwayo da Feng Yuanzheng ya nuna a cikin kafar televition mai suna "Kada ka yi magana da wanda ba ka san shi sosai ba, Mr Feng Yaunzheng ya dauki matsatin wani likita mai suna An Jiahe wanda bai amince da amaryarsa da ta gamu da wulakancin jima'in da aka yi mata tilas ba, sa'anan ya dake ta ba ji ba gani. Abubuwan da ya yi a cikin wasan sun yi daidai da abubuwan da suke faruwa a cikin zaman rayuwa na yau da kullum sosai da sosai , har ma wasu 'yan kallo ba su iya bambance abubuwan da ya nuna a cikin wasan da zaman rayuwarsa na yau da kullum ba. A wani lokacin da yake cin abinci a cikin wani dakin cin abinci, ba zato ba tsammani wata tsohuwa ta zuwa wurin da ya zauna, ta mare shi , sa'anan ta gaya masa cewa, kada ya dinga yi wa matarsa wulakanci, wannan ya sanya wa Feng Yuanzheng rashin jin dadi sosai.

Mai jagorar wasan ya bayyana cewa, da farko, ba a zabi Feng Yunzhen da ya zama manyan 'yan wasa a cikin wasan ba, amma, wadanda aka zabe su don su zama babban dan wasa a cikin wasan sun nuna damuwarsu a kan wasan da ke iya lalata sifofinsu, shi ya sa suka ki karbar kwangilar nuna wasan, amma Feng Yuanzhen bai lura da wannan ba, ya karbi wasan, ya nuna wasan cikin jaruntaka. Bayan nuna wasan ga 'yan kallo a fili , sai aka mayar da shi bisa matsayin mugun namiji. Game da wannan , Mr Feng Yaunzheng ya bayyana cewa, bisa matsayin dan wasa, a wani lokaci, bai kamata ba ka lura da sunanka sosai . Ya ce, dalilin da ya sa na karbi wasan, shi ne saboda abubuwan da ke cikin wasan ya burge ni sosai da sosai. Idan wasan bai burge ni sosai ba, to ba na iya karbar wasan , ko da akwai kudi da yawa da za aba ni.

1 2 3