Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-05 22:25:16    
Tabkin Lu Gu Hu mai kyan gani

cri

A yayin da mutum yin yawo a kewayen tabkin Lu Gu Hu, zai iya ganin ruwan tabkin Lu Gu Hu da sararin sama su zama kamar gu daya. A duk lokacin da ake rana, ana iya ganin sararin sama da gajimare a cikin ruwan tabkin. Tabkin Lu Gu Hu ya yi kama da lu'ulu'un da aka ajiye a tsakanin manyan tsaunuka.

Baya ga ruwa mai tsabta na tabkin Lu Gu Hu, tsibiran da ke cikin wannan tabki na da kyan gani kwarai. Wadannan tsibirai suna kama da kwale-kwale masu launin kore da ke tafiya a kan tabkin. A cikinsu, tsibiran Hei Wa WU da Li Wu Bi da kuma Li Ge sun fi gamsuwa ga matafiya wajen kai ziyara. Ana kiran wadannan tsibirai 3 'tsibirai 3 na Peng Lai', wato tsibirai 3 da ke cikin aljanna.

Tsibirin Hei Wa Wu na kasancewa cibiyar tabkin Lu Gu Hu, yana da nisan mita 2500 a tsakaninsa da kauyen Luo Shui da ke gabar tabkin. A kan samu dimbin itatuwa da tsuntsaye a kansa. Shi wuri ne na hutawa da tsuntsayen da ke kaiwa da kawowa a kudancin kasar Sin da arewacin kasar su kan yada zango a kai.

Shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Lu Gu Hu ta kan jawo masu yawon shakatawa masu tarin yawa da suka zo daga sassa daban daban na duniya bisa ni'imtattun wurare da kuma al'adun kabilar Mosuo masu cikakken bambanci da mata suke mallakar kusan kome da kome. Amma a shekarun baya da suka wuce, wannan kyakkyawar shiyyar yawon shakatawa mai ban mamaki ta gamu da mummunar illa a sakamakon raya ta. An raunana kyakkyawan muhallin wurin.

Saboda haka, hukumar lardin Yunnan ta gudanar da aikin kyautata muhalli a gabar tabkin Lu Gu Hu, wanda ya kyautata yanayin tabkin da kuma muhallin da ke kewayen tabkin sosai. Sa'an nan kuma, aikin ya ba da tasiri ga 'yan kabilar Mosuo da ke zaune a dab da wannan tabki daga zuriya zuwa zuriya. Lu Zu, mai shekaru 18 da haihuwa, dan kabilar Mosuo, an haife shi ne a kewayen tabkin Lu Gu Hu, inda kuma ya girma. Bayan da ya gama karatu a makarantar sakandare, ya fara tuka matafiya a cikin kwale-kwale a gabar tabkin. Wannan sauraryi ya gaya mana cewa,"Matafiya su kan gurbata muhalli. Shi ya sa muke yin kira gare su da kada su jefa shara barkatai a ciki. Ban da wannan kuma, mu kanmu wajibi ne mu kiyaye wannan tabki domin samun bunkasuwa mai dorewa."

Ya zuwa yanzu 'yan kabilar Mosuo suna bin al'adar gargajiya, wato mata ne suke mallakar kusan kome da kome. Kaka mace ita ce shugabar ko wane iyali. A ko wane iyali, akwai wani dakin musamman da ake gina wa kaka mace. Ana yi wa wannan daki ado ta hanyar musamman. Wannan daki yana matsayin cibiyar wannan iyali ne ga dukkan mambobin iyalin. A shekarun baya, a sakamakon tasirin al'adun da ba na kabilar Mosuo ba, yawan dakunan da 'yan kabilar Mosuo suke gina wa kakanni mata na ta raguwa. Al'adun kabilar Mosuo mai cikakken bambanci wato kakanni mata suna mulkin iyalai na bacewa a kwana a tashi. Dan haka, kwamitin kula da tabkin Lu Gu Hu ya dauki matakai cikin himma domin kiyaye al'adun kabilar Mosuo da ake samu a tabkin Lu Gu Hu kawai. Ya karfafa gwiwar 'yan kabilar Mosuo da su gina wa kakanni mata dakunan musamman, su yi amfani da kayayyakin gine-gine da suka saba yin amfani da su, su bi hanyar gargajiya da suka saba bi, ta haka salon gine-gine na wadannan dakunan musamman ba zai canza ba. Yu Li Jun, darektan kwamitin kula da tabkin Lu Gu Hu ya yi karin bayanin cewa,"Al'adun kabilar Mosuo al'adu ne masu cikakken bambanci a duniya, kuma ba za a iya maye gurbinsu ba. Iyalan 'yan kabilar Mosuo suna matsayin abu mafi muhimmanci na al'adun wannan kabila, wanda mata suke mallakar kusan kome da kome. Ba za mu iya kiyaye al'adun kabilar Mosuo wadanda ba na kaya ba, sai da farko mun iya kiyaye abubuwan al'adun wannan kabila yadda ya kamata. In mun rasa abubuwan al'adu da muke iya taba su, to, yau da gobe za mu iya rasa wadannan al'adu."


1 2 3