Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-05 22:25:16    
Tabkin Lu Gu Hu mai kyan gani

cri

Da akwai tsibirai 5 da mashigai 3 da kuma wani tsibirin da ya hada babban yanki gu daya a cikin tabkin Lu Gu Hu. Ko da yake siffofin wadannan tsibirai na shan bamban da juna, amma dukkansu akwai itatuwa da yawa a kansu. Ana tukin kwale-kwale sannu sannu a kan takbin tare da sauraren wakokin 'yan kabilar Mosuo masu dadin ji. Akwai yanayi na tsit a tabkin Lu Gu Hu.

Tabkin Lu Gu Hu tabki ne mafi tsayi daga leburin teku a lardin Yunnan, haka kuma, daya ne daga cikin tabkuna mafiya zurfin bakin ruwa a kasar Sin. Itatuwa masu launin kore da ruwan tabkin mai launin shudi sun hade da juna, har ma sun fito da wani zane mai kyan gani. A wasu tsibirai, an gina gidan ibada na addinin Buddha na gargajiya na Tibet, inda 'yan kabilar Mosuo kan durkusa a gaban mutum-mutumin addinin Buddha.

Tabkin Lu Gu Hu yana kewaye da manyan tsaunuka. A kan samu dusar kankara a kansu a watanni fiye da 3 a ko wace shekara. A kewayen tabkin, 'yan kabilun Mosuo da Yi da Han da Naxi da Tibet da Pumi da Bai da kuma Zhuang kimanin dubu 13 suna zama tare cikin lumana, ciki har da 'yan kabilar Mosuo kimanin dubu 6. A shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Lu Gu Hu, ni'imtattun wurare irin na tudu da na tabki da kuma al'adun kabilar Mosuo masu cikakken bambanci da mata suke mallakar kusan kome da kome sun fi jawo hankalin mutane. A shekarar 1993, lardin Sichuan ya kebe tabkin Lu Gu Hu a matsayin shiyyar yawon shakatawa ta lardin.

He Yuhong, wanda ya zo tabkin Lu Gu Hu ziyara daga birnin Guangzhou, ya yaba da kyan ganin wannan tabki sosai, inda ya ce,"Wurare na da ni'ima matuka, musamman ma ruwa. Ruwan tabkin na da tsabta, har ma muna iya ganin gindin tabkin. Mun taba ganin wasu kananan dabbobi suna zagayawa a cikin ruwan."

1 2 3