Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-05 22:25:16    
Tabkin Lu Gu Hu mai kyan gani

cri

A bakin iyakokin lardunan Yunnan da Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin, akwai wani kyakkyawan tabki mai suna Lu Gu Hu, inda a kewayensa, aka tsugunar da 'yan kabilar Mosuo, wadanda ya zuwa yanzu mata suke mallakar kusan kome da kome. Al'adun kabilar Mosuo mai dogon tarihi da ni'imtattun wurare da kuma 'yan kabilar Mosuo masu ban mamaki suna jawo hankalin mutane sosai. Sa'an nan kuma, tabkin Lu Gu Hu da 'yan kabilar Mosuo suke dogaro gare shi ya fi jawo hankalin mutane. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku karin bayani kan wannan kyakkyawan tabkin na Lu Gu Hu.

Fadin tabkin Lu Gu Hu ya wuce murabba'in kilomita 50. Matsakaicin zurfin ruwan tabkin ya kai mita 45, zurfin ruwan tabkin mafi zurfi ya wuce mita 90, haka kuma, ana iya ganin abubuwan da ke cikin tabkin har na zurfin mita 11. Tabkin Lu Gu Hu yana kasancewa wurin da ke da tsayin mita 2690 daga leburin teku. A da, ana kiran tabkin Lu Gu Hu 'Lu Ku Hai Zi' ko kuma 'Zuo Suo Hai' ko kuma 'Liang Hai'. A bakin 'yan kabilar Mosuo, ma'anar tabkin Lu Gu Hu ita ce tabkin da ke cikin kwari.

1 2 3