Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-05 16:51:20    
MDD ta kira taron musamman kan batun cutar mura mai nau'in A(H1N1)

cri

Sakamakon ci gaba da yaduwar cutar mura mai nau'in A(H1N1) a dimbin kasashe da yankuna a duniya, hakan ya jawo hankalin gwamnatoci da jama'ar kasashe daban daban sosai, shi ya sa a karshen makon jiya, MDD ta tsai da kuduri kan kira taron musamman kan cutar. Madam Margaret Chan, babbar darakta ta kungiyar WHO ita ma ta bayyana a taron ta akwatin talibijin a Geneva. Kuma ta bayyana cewa, "Ya zuwa yanzu ba mu san yaushe ne za mu daga matsayin shirin-ko-ta-kwana na cutar zuwa matsayi na shida ba, wanda ya shaida barkewar cutar a duk fadin duniya sosai, amma yanzu halin da ake ciki bai tsananta kamar haka ba. Idan an samu alamar yaduwar cutar tsakanin mutane da mutane a sauran wurare ban da arewacin Amurka, to za a kara matsayin shirin-ko-ta-kwana."

Wakilan kasashe membobin MDD su ma sun yi jawabi bi da bi don bayyana aniyar yakar cutar da kuma matakan da suke dauka, a waje daya kuma sun nuna goyon baya sosai ga ayyukan da MDD musamman ma kungiyar WHO ke gudanarwa kan fama da cutar.(Kande Gao)


1 2 3