Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-05 16:51:20    
MDD ta kira taron musamman kan batun cutar mura mai nau'in A(H1N1)

cri

Ban da wannan kuma Ban Ki-monn ya jaddada a yayin taron, cewar wannan cutar da ta shafi kasashe da yankuna daban daban ta sake yi wa mutane gargadin cewa, kwayoyin cuta za su iya yaduwa a ko wace kasa ba tare da nuna zabi ba, shi ya sa ya kamata a hada gwiwa sosai don yin yaki da su, wato ba kawai a yi la'akari da moriyar wata kasa ba, hatta ma a daidaita batun a matsayin bunkasuwar duniya gu daya. Kuma ya kara da cewa, "Ya kamata mu yi la'akari da moriyar kanmu da kuma kwanciyar hankalin duniya tare yayin da muke fama da cutar mura mai nau'in A(H1N1), kuma wannan ita ce wata jarrabawa da aka yi wa duk dan Adam. Ya kamata mu tinkari cutar ta hanyar hadin gwiwarmu tsakanin bangarori da yawa cikin yakini, da kuma tallafa wa kasashen da ke bukatar taimakon agaji musamman ma kasashe masu tasowa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da watakila za su yi fama da wahalhalu sosai wajen fuskantar wannan kalubale. Haka kuma muddin an yi haka, to za a iya tabbatar da kiwon lafiyar jama'ar kasashe daban daban."

1 2 3