Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-05 16:51:20    
MDD ta kira taron musamman kan batun cutar mura mai nau'in A(H1N1)

cri

A ran 4 ga wata, MDD ta kira taron musamman don tattaunawa kan cutar mura mai nau'in A(H1N1) da ke jawo hakalin kasashe daban daban yanzu. Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi jawabi a yayin taron, inda ya yi kira ga kasashe daban daban da su ci gaba da sanya muhimmanci da yin hattara da ci gaban halin da cutar ke ciki, da kuma mai da hankali kan labaran da kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ke bayarwa. To yanzu ga cikakken bayani.

A yayin taron musamman da MDD ta kira kan cutar mura mai nau'in A(H1N1), Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kira taron cikin lokaci ya zama wajibi. Yanzu mutane ba su san dimbin abubuwa kan cutar ba, kuma ba su fahimci hadarin da cutar za ta iya kawowa ba. Sabo da haka ya ce,"bai kamata ba mu tashi hankali sosai sakamakon dimbin labaran da kafofin watsa labarai ke bayarwa kan cutar mura mai nau'in A(H1N1), a waje daya kuma bai kamata ba mu dauki cutar cikin sauki sakamakon raguwar yawan labaran da aka bayar. A cikin halin kasancewar dimbin abubuwan da ba su tabbata ba, dole ne mu yi hattara da cutar a ko yaushe, mu kuma lura da labaran da kungiyar WHO ke bayarwa kan cutar."

1 2 3