Tare da samun bunkasuwar jihar Tibet daidai da zamani cikin sauri, gwamnatin kasar Sin tana rubanya kokarinta wajen aiwatar da muhimman tsare-tsare na zabar nagartattun mahukunta 'yan kananan kabilu da horas da su a fannin kimiyya da fasaha. A halin yanzu, mahukunta da masu ilimin kimiyya da fasaha 'yan kabilar Tibet sun kasance ginshikai a fannin raya jihar Tibet. Wani manazarci na cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta jihar Tibet mai suna Kelzang Yeshe ya ce:"A cikin shekaru 50 da suka gabata da aka yi gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet, an samu manyan sauye-sauye a jihar. Tsohon tsarin bautawa iyayen gijin bayi da aka shafe tsawon shekaru 300 ko fiye ana yinsa ya canja kwarai da gaske. Idan ba'a yi gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet ba, zaman rayuwar mazauna jihar ba zai kyautata ba.
To, masu saurare, mun kawo muku bayani na musamman dangane da muhimman sauye-sauyen zaman rayuwar jama'ar jihar Tibet a cikin shekaru 50 da suka wuce. A cikin shirinmu na nan gaba, za mu cigaba da maida hankali kan zaman jin dadi da jama'ar jihar Tibet suke ciki. Yanzu sai ku dan shakata kadan, daga bisani za mu dawo domin kawo muku wasu labarai dangane da kananan kabilun kasar Sin. 1 2 3
|