Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-04 21:52:48    
Sauye-sauyen zaman rayuwar mazauna jihar Tibet a cikin shekaru 50 da suka gabata

cri

Aiwatar da tsarin cin gashin kai a yankin kananan kabilu cikin himma da kwazo, yana karfafa ikon 'yan kananan kabilu a jihar Tibet na shiga cikin harkokin siyasa da bada shawarwarinsu. A halin da ake ciki yanzu, a cikin 'yan majalisar wakilan jama'ar jihar sama da 34000, akwai 'yan kabilar Tibet da na sauran kananan kabilu wadanda yawansu ya zarce kashi 94 bisa dari. Yayin zaman taron majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet, 'yan majalisar bisa matakai daban-daban sun bayar da shawarwari masu dimbin yawa a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu, da zamantakewar al'umma, wadanda suka bayar da babbar gudummawa wajen daukaka cigaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar mazauna jihar.

Kamar yadda mataimakin darektan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet A Teng ya bayyana cewa:"'Yan kabilar Tibet da na sauran kananan kabilu sun nuna hazaka sosai wajen gudanar da ikonsu a fannin siyasa. A cikin zabubbukan 'yan majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet bisa matakai hudu da suka gudana a shekara ta 2007, yawan mutanen da suka halarci zabubbukan ya kai kashi 96.4 bisa dari, har ma ya kai kashi 100 bisa dari a wasu wurare a jihar."

1 2 3