Yayin da ake yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet, ba ma kawai zaman rayuwar mazauna jihar ya kyautata ba, har ma sun kara samun ikon gudanarwa ta fannin dimokuradiyya. A shekara ta 1961, an fara gudanar da zabubbuka a wurare daban-daban na jihar, wadanda suka baiwa 'yantattun bayi manoma masu dimbin yawa damar zama shugabanni bisa matakai daban-daban a jihar.
A watan Satumban shekara ta 1965, an kaddamar da babban taron majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet a karo na majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet A Teng ya ce:"Zaman taro na farko na majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet mai cin gashin kanta a karo na farko da aka shirya a watan Satumba na shekara ta 1965, ya alamanta cewa, Tibet ta fara aiwatar da tsarin cin gashin kai a yankinta. A gun taron, an zabi 'yan kwamitin jama'a na jihar ta hanyar jefa kuri'a. Daga wannan lokaci ne, aka samu hukumomin kula da harkokin cin gashin kai a jihar Tibet, wato majalisar wakilan jama'ar jihar, gami da kwamitin jama'a."
Bayan da aka fara aiwatar da tsarin cin gashin kai a jihar Tibet, jihar ta samu manyan sauye-sauyen da ba'a taba ganin irinsu ba a tarihi a fannonin tattalin arziki, da al'adu, tare kuma da zaman rayuwar jama'a. A farkon shekarun 1980 na karnin da ya gabata, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta fitar da manufofi da dama don tallafawa manoma da nuna musu gatanci, ciki har da raya sabbin kauyuka, da gudanar da tsarin bada hidimar aikin jinya ga manoma ba tare da biyan kudi ba, ta yadda manoma da makiyaya wadanda adadinsu ya zarce kashi 80 bisa dari na dukkan jama'ar jihar Tibet suka cimma moriya.
1 2 3
|