Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-04 17:29:01    
Kasar Sin ta bayar da shirin daidaita shirin bunkasa tattalin arziki a fannoni 10

cri

Masana sun kuma bayyana cewa, ban da tabbatar da fama da matsalar hada hadar kudi ta duniya da samar da isassun guraban aikin yi, ana kuma sa ran cewa za a iya samun ci gaban wadannan sana'o'in cikin dogon lokaci mai zuwa. Musamman an sa kaimi ga masana'antu da su iya kirkiro sabbin fasahohin zamani da kansu da kuma raya tamburan kayayyakinsu a kasuwa. Alal misali, gwamnatin tsakiya za ta zuba karin jari kan sana'ar kera jiragen ruwa domin kara karfin kirkiro sabbin fasahohin zamani na kera jiragen ruwa na zamani. Bugu da kari kuma, za a kebe kudin musamman da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 10 domin raya sana'ar kera motoci. Mr. Guo Tongjun, wani direktan sashen rukunin kera manyan jiragen ruwa na kasar Sin ya ce, "Cikin daidai lokaci ne aka daidaita shirin farfado da masana'antun kera jiragen ruwa a gare mu. Muna da imani cewa, bayan da aka bayar da wannan shiri da wasu manufofi da matakai da suke da nasaba da wannan shiri, tabbas ne kasarmu za ta iya kara saurin cimma burinta na zama wata babbar kasar mai wadata wadda ke da karfin kera manyan jiragen ruwa."

Haka kuma, Mr. Jin Gebo, mataimakin babban direktan kamfanin sayar da mota kirar Chery na kasar Sin ya bayyana cewa, bayan da aka bayar da wadannan manufofin nuna goyon baya, kamfaninsa yana cike da imani ga kasuwar mota kirar Chery a shekara ta 2009. Mr. Jin ya ce, "Wadannan manufofin da gwamnati ta bayar za su cika imanin masu saye-saye. A waje daya kuma, za mu fitar da wasu motoci na sabon salo. Mun yi hasashen cewa, a shekara ta 2009, yawan motocin da za mu iya sayarwa a kasuwa zai kai tsakanin kashi 5 cikin kashi dari zuwa kashi 12 cikin kashi dari."

Manazarta sun nuna cewa, wadannan shirye-shirye 10 suna kuma habaka bukatu a cikin kasuwar kasar Sin domin sa kaimi ga kokarin canja karuwar tattalin arzikin kasar. Amma, kasar Sin ba za ta dauki matakan kariya cinikin waje ba. Mr. Liu Tienan, mataimakin shugaban kwamitin neman ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya ce, "Babu abubuwan kariya cinikin waje ba a cikin wadannan shirye-shiryenmu. Muna fatan masana'antunmu za su iya samun karfin yin takara a kasuwa ta hanyar yin takara a kasuwa cikin adalci. Bugu da kari kuma, bisa ka'idojin wadannan shirye-shirye, za mu kara saurin daidaita tsarin sana'o'inmu domin cimma burinmu na karfafa karfinsu." (Sanusi Chen)


1 2 3