Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-04 17:29:01    
Kasar Sin ta bayar da shirin daidaita shirin bunkasa tattalin arziki a fannoni 10

cri

Masana sun ce, bayan da an sassauta nauyin da ke kan masana'antu, za a iya samun sassauci kan batun samar da guraban aikin yi da yake ta tsananta yanzu. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, ya zuwa farkon shekarar 2009, yawan manoma 'yan ci rani da suka rasa guraban aikin yi a birane ya kai kimanin miliyan 20. Sana'o'in saka da samar da kananan kayayyakin masarufi da na kera injuna su ne muhimman sana'o'in da ke iya samar da guraban aikin yi ga manoma 'yan ci rani. Sakamakon haka, shirye-shiryen farfado da muhimman sana'o'i goma za su iya taka rawa wajen kyautata halin da ake ciki a kasar Sin wajen samar da guraban aikin yi.

Sakamakon matsalar hada hadar kudi ta duniya, wasu masana'antun kasar Sin sun shiga cikin mawuyacin hali wajen tafiyar da harkokinsu. Wannan kuma ya bayyana cewa, ya kasance wasu matsaloli a cikin tsarin masana'antu na kasar Sin. Alal misali, yanzu yawan kamfanonin samar da bakin karfe kanana ko manya ya kai kimanin 1200, daga cikinsu yawan manya da matsakaitan kamfanonin bakin karfe ya kai kimanin 70. Wadannan adadi ya bayyana cewa, yawan masana'antun bakin karfe ya yi yawa. Kuma suna takara da juna cikin ruda. Sakamakon haka, yawan ribar da suke samu ya yi kadan. Sabo da haka, Mr. Luo Bingsheng, mataimakin shugaban kungiyar masana'antun bakin karfe ya bayyana cewa, a shekara ta 2008, an riga an hada wasu masana'antun bakin karfe, kuma an riga an soma yin takara a tsakanin manyan rukunonin bakin karfe.

"Yawan danyen bakin karfe da kamfanonin bakin karfe mafi girma 10 suka samar ya kai ton miliyan 210, wato ya kai kashi 42.5 cikin kashi dari bisa na dukkan danyen bakin karfe da aka samar a kasar Sin a shekara ta 2008, kuma ya karu fiye da kashi 5 cikin kashi dari bisa na shekara ta 2007."

Mr. Zhu Hongren, wani jami'in ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, ana fatan za a iya kara saurin daidaita tsarin sana'o'in a yankuna daban daban kamar yadda ya kamata. Sakamakon haka, za a iya samun wasu manyan kamfanonin da suke da karfin yin takara sosai. Mr. Zhu ya ce, "Wadannan shirye-shiryen farfadowa da muhimman sana'o'i goma sun sa kai, da kuma ba da jagoranci ga masana'antu da su hada kan juna ta hanyar tsarin kasuwanci. Sakamakon haka, za a iya samun wasu manyan rukunonin masana'antu wadanda suke da karfin yin takara sosai a kasuwannin duniya."

1 2 3