Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-04 17:29:01    
Kasar Sin ta bayar da shirin daidaita shirin bunkasa tattalin arziki a fannoni 10

cri

Tun daga ran 14 ga watan Janairu zuwa ran 25 ga watan Faburairu, wato a cikin kwanaki 40 da wani abu kawai, bi da bi ne gwamnatin kasar Sin ta bayar da tsarin daidaita shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki a fannoni 10, wato sana''ar motoci da ta bakin karfe da ta saka da ta samar da injunan zamani da ta kera jiragen ruwa da yanar gizo da ta sadarwa da ta man fetur da ta sufurin kayayyaki da dai makamatansu. Masana sun bayyana cewa, wadannan shirye-shirye 10 za su taka rawa sosai wajen daidaita matsalolin da ke kasancewa a gaban masana'antun kasar Sin, da kuma kyautata fasahohin wadannan sana'o'i da kuma kyautata tsarin tattalin arziki.

Game da wadannan sana'o'i goma na kasar Sin, Mr. Liu Tienan, mataimakin shugaban kwamitin neman ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya ce, wadannan sana'o'i suna kan matsayi mafi muhimmanci a cikin tattalin arzikin kasar. Mr. Liu ya ce, "Yawan mutanen da suke aiki a wadannan sana'o'i goma ya kai fiye da miliyan dari 1. A waje daya kuma, yawan kudaden GDP da muka samu da yawan masana'antun da suke cinikin takardun hannu jari a kasuwa ya kai kashi 60 cikin kashi dari daga cikin dukkan masana'antun kasar Sin su masana'antu ne daga wadannan sana'o'i goma. Sakamakon haka, idan aka iya tabbatar da ci gaban wadannan sana'o'i goma, za a iya ba da tabbaci ga kasafin kudi da kudaden harajin da ake bugawa da yawan guraban aikin yi da kuma batutuwan da suke da nasaba da aikin gona da kauyuka da manoma."

Lokacin da ake tinkarar hada hadar kudi a duk duniya, yawan kayayyaki kirar kasar Sin da ake bukata a kasuwannin kasashen waje ya ragu. Sakamakon haka, yawan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje daga kasar Sin ya ragu cikin sauri. Lokacin da ake bayar da shirye-shiryen kara saurin raya wadannan sana'o'i 10, kasar Sin ta soma daukar matakai cikin hali mai yakini domin tabbatar da karuwar tattalin arzikin sana'o'in samar da injuna da saka da bakin karfe da kuma masana'antun da ke samar da kayayyakin masarufi. Bisa matakan da aka dauka, za a kara samar da rancen kudi ga masana'antun da suke cikin mawuyacin hali wajen yin kayayyakinsu yanzu. Kuma za a kara mayar da harajin kwastan ga masana'antun da suke fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje.

Alal misali, tun daga watan Janairu zuwa watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, jimillar ribar da manyan masana'antun saka na kasar Sin suka samu ta ragu. Shi ne karo na farko da suka rasa samun riba a cikin shekaru 10 da suka gabata. Sabo da haka, Mr. Sun Huaibin, kakakin kungiyar masana'antun saka ta kasar Sin ya ce, bayan da aka bayar da shirin farfadowa da masana'antun saka, za a kara karfin taimakawa masana'antun saka a fannonin kasafin kudi. Shi ne wani kyakkyawan lamari ga masana'antun saka wadanda suke cikin mawuyacin hali yanzu. Mr. Sun ya ce, "Wannan mataki zai taka rawa wajen taimakawa masana'antu wadanda suke cikin mawuyacin hali kan kokarin samun jari. Bayan da bankuna suka aiwatar da manufofin kasafin kudi da haraji lokacin da suke ba da rancen kudi ga masana'antu, za a iya biyan bukatun da masana'antu ke nemawa a fannonin samun kudaden aiwatar da harkokin kawo albarka."

1 2 3