A waje guda kuma, manyan jami'an sojojin ruwa na kasashe daban-daban dake halartar bukin sun nuna babban yabo ga wannan lamari. Janar Noman Bashir, babban hafsan-hafsoshin sojan ruwa na kasar Pakistan ya ce: "Yankin teku, ba mallakin wata kasa ba ne daya tilo, amma mallakin kasashen duniya ne daban-daban. Kowace kasa tana da bukatarta a fannin yin amfani da albarkatun teku, shi ya sa, idan dukkanin kasashe za su iya shimfida zaman lafiya da neman bunkasuwa a yankin teku, za'a shimfida zaman lafiya a duk duniya."
Kafin bukin duba faretin sojojin ruwan, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da shugabannin tawagogin kasashe daban-daban wadanda suka zo don halartar bukin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta nace ga bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, ko a halin yanzu, ko kuma a nan gaba, kasar Sin ba za ta nuna isa ba a duniya.(Murtala) 1 2 3
|