Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-24 19:15:24    
A karo na farko kasar Sin ta shirya bukin duba faretin sojojin ruwa na hadin-gwiwar kasashe daban-daban

cri

Mataki na biyu kuwa shi ne, bukin duba faretin sojojin ruwa a yankin teku. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya duba faretin jerin gwanon jiragen ruwa yaki guda 21 na kasashe 14 karkashin jagorancin jirgin ruwan yaki mai dauke da makamai masu linzami kirar "Xining" na kasar Sin, ciki har da jirgin ruwan yaki kirar "Varyag" na kasar Rasha, da jirgin ruwan yaki kirar "Fitzgerald" na Amurka da dai sauransu.

A cikin tsawon kwanaki 4 da suka gabata, sojojin ruwa na kasashe daban-daban sun hadu a birnin Qingdao na kasar Sin, inda suka yi shawarwari, da musanyar ra'ayoyi da juna, haka kuma, sun shirya wasanni iri-iri, da kallar bukin nune-nunen nasarorin da aka samu a fannin raya birnin Qingdao, gami da kai ziyara ga wuraren yawon shakatawa a birnin, ta yadda sojojin ruwa na kasashe daban-daban za su kara fahimtar juna, da yaukaka dankon zumunci da fadada hadin-gwiwa a tsakaninsu. Janar Wu Shengli, kwamandan rundunar sojan ruwa ta kasar Sin ya nuna cewa: "'Wanzar da zaman lafiya mai dorewa, da raya duniya mai wadata', sanarwa ce da gwamnatin kasar Sin ta bayar, haka kuma babban burin shirya wannan buki shi ne 'shimfida zaman lafiya, da inganta hadin-gwiwa a yankin teku'. Kasar Sin ta shirya wannan buki tare da zummar inganta mu'amala da cudanya tsakanin sojojin ruwa na kasashe daban-daban, ta yadda za su kara fahimtar kasar Sin gami da sojojin ruwanta."

1 2 3