Domin murnar cika shekaru 60 da kafa rundunar sojan ruwan kasar Sin, a ranar 23 ga wata da maraice, a yankin teku dake dab da birnin Qingdao na kasar Sin ne, aka yi bukin duba faretin jiragen ruwan yaki na hadin-gwiwar kasashe daban-daban. Shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar Hu Jintao ya duba faretin jiragen ruwan yaki, da jerin gwanon jiragen sama na kasar Sin, gami da jiragen ruwan yaki na kasashe daban-daban da suka halarci bukin bisa goron gayyatar da aka ba su. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta shirya bukin duba faretin sojojin ruwa na hadin-gwiwar kasashe daban-daban, wanda kuma ya fi girma a tarihi.
Da misalin karfe 2 na yammacin ranar 23 ga wata ne, shugaba Hu Jintao ya isa yankin teku da za'a yi bukin. Da karfe 2 da minti 20 ne, bayan da Hu Jintao ya bada umurni, aka kaddamar da bukin duba faretin sojojin ruwa na kasar Sin da jiragen ruwan yaki na kasashe daban-daban.
Bukin duba faretin sojojin ruwa da aka shirya a wannan gami ya kasu gida biyu. Da farko dai, daya bayan daya ne Hu Jintao ya duba faretin jiragen ruwan yaki dake tafiya a karkashin ruwa, da jiragen ruwa masu aikin bada kariya, da dai sauran jiragen ruwan yaki, tare kuma da ayarin sojojin sama na rundunar sojan ruwan kasar Sin.
1 2 3
|