Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-23 14:29:06    
IMF na sa ran farfado da tattalin arzikin duniya a shekara mai kamawa

cri

Jama'a masu saurare, wannan rahoto da IMF ya gabatar ya nuna cewa, kasashe daban-daban na duniya za su samu raguwar bankasar tattalin arziki a wannan shekara da kashi 1.3 cikin kashi 100 da ba ta taba ganin kamar irinta ba tun babban yakin duniya na biyu duk da wassu alamu masu faranta rai da aka samu bayan taron koli na G20 kan tattalin arzikin duniya da aka gudanar a London. Rahoton ya jaddada cewa, dole ne a dogara kan maido da kyakkyawan tsarin kudi na duniya yayin da ake habaka bukatu ta hanyar yin amfani da kudi.

A karshe dai, rahoton ya yi kira ga gwmnatocin kasashe daban-daban da su aiwatar da tsauraran manufofin tattalin arziki a cikin gida yayin da suke kara yin hadin gwiwa tare da kasashen waje. Idan sun dauki matakan da suka kamata, to labuddah za su samu farfadowar tattalin arziki a shekara mai kamawa duk da kasancewar wassu matsaloli da suke fama da su. (Sani Wang)


1 2 3