Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-23 14:29:06    
IMF na sa ran farfado da tattalin arzikin duniya a shekara mai kamawa

cri

An labarta cewa, asusun bada lamuni na IMF ya bayar da wani sabon rahoto dake da lakabi haka : ' Hangen tattalin arzikin duniya', wanda ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya ya rigaya ya samu koma baya mai tsanani tun bayan yakin duniya na biyu, wato ke nan tattalin arzikin duniya na wannan shekara zai samu raguwa da kashi 1.3 cikin kashi 100. Bisa wannan hali dai a cewar rahoton, idan kasashe daban-daban suka dauki tsauraran matakai na sa kaimi, to ana sa ran samun farfadowar tattalin arzikin duniya sannu a hankali nan da shekarar 2010 kana ana kyautata zaton cewa tattalin arizikin duniya zai samu karuwa da kashi 1.9 cikin kashi 100.

Jama'a masu saurare, wannan sabon rahoto na bayyana cewa, rikicin hada-hadar kudi da kuma koma bayan tattalin arzikin duniya sun yi babbar illa ga tattalin arzikin shiyyoyi daban-daban na duniya, wadanda kusan daukacinsu suka samu raguwar tattalin arziki da ta yi kasa da ta tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007 ; Ban da wannan kuma, matsakaicin yawan kayayyakin da kowane mutum na kasashen da suka dauki kashi uku cikin kashi hudu bisa adadin tattalin arzikin duk duniya zai samu raguwa, musamman ma kasashen da suka fi samun bunkasuwar tattalin arziki sun kasance tamkar wata shiyyar dake gamuwa da babban bala'i.

1 2 3